Ɗan Takarar Gwamna daya sha kaye a Zaɓen Fidda Gwani Sha’aban, yasha alwashin marawa Sanata Uba Sani baya

0

Ɗan Takarar Gwamna daya sha kaye a Zaɓen Fidda Gwani Sha’aban, yasha alwashin marawa Sanata Uba Sani baya - Dimokuradiyya

Ɗan Takarar Gwamna daya sha kaye a Zaɓen Fidda Gwani Sha’aban, yasha alwashin marawa Sanata Uba Sani baya

A Jihar Kaduna bayan Kwanaki da kammala zaɓen fidda gwani na Gwamna a jam’iyar APC, Hon Sani Sha’aban yasha alwashin taimakawa Sanata Uba Sani a Babban zaɓen Shekarar 2023 Mai zuwa, domin ganin ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kaduna.

Sanata Uba sani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai ɗauke da Hoton sa tare da Sani Sha’aban a lokacin daya Kai ziyara Gidan Sani Sha’aban.

Sanata Uba sani yace “A jiya na ziyarci ɗan uwana kuma ɗan takara a zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Hon. Mohammed Sani Sha’aban munyi musayar ra’ayoyi da dabaru kan yadda za a tabbatar da nasarar jam’iyyar mu a zaben gwamnan jihar Kaduna na 2023.

Hon Sha’aban Shahararren mai dabarar siyasa kuma mai wayar da kan jama’a, Sha’aban, ya tabbatar min da cewa zai yi amfani da fasaharsa ta siyasa da dimbin hanyoyin sadarwarsa don ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen 2023 a jihar Kaduna.

Uba sani Ya Kara da cewa “Ɗan siyasar da ake mutuntawa bayan ya yi alkawarin goyon bayana a zaben gwamna ya kuma tabbatar da zai hada kan Al’umma domin ganin mun mamaye gidan Kashim Ibrahim a 2023.

“Mun kuma amince da ƙulla alaƙa mai ɗorewa domin ci gaba da ci gaban jihar Kaduna wacce ke da tushen tarihin wadata da kuma hadin kai musamman domin tabbatar da turbar Gwamna El-Rufai a jihar Kaduna.

“Ganawar tamu ta kasance mai daɗi da amfani. Alamar manyan abubuwan da zasu zo a cikin jihar mu. Na gode Hon. Sha’aban”. Inji Sanata Uba Sani.

Sanata Uba sani shine Dan takarar Gwamnan jihar kaduna Karkashin jam’iyar APC yanzu haka.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy