Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna, Uba Sani ya taya Tinubu murnar lashe Zaɓen APC

0

Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna, Uba Sani ya taya Tinubu murnar lashe Zaɓen APC - Dimokuradiyya

Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna, Uba Sani ya taya Tinubu murnar lashe Zaɓen APC

Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya taya tsohon Gwamnan Jahar Lagos Bola Ahmed Tinubu murnar lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar, data shirya.

Sanata Uba Sani ya faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa daya fitar domin taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen Fidda Gwani na jam’iyar APC.

Sanata Uba Sani wanda ya kasance Ɗan Takarar Gwamnan jihar Kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, yana Mai cewa “nima bari in bi Sahun miliyoyin masoya jam’iyyar mu da masu fatan alheri a Najeriya da ma duniya baki ɗaya wajen taya fitaccen ɗan siyasar mu kuma ƙwararre a harkokin siyasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a zabyen fidda gwanin takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC a Abuja”.


Download Mp3

“Nasarar da Asiwaju ya samu, jam’iyyar APC wani yunƙuri ne na yiwa PDP da sauran jam’iyyu ritaya a babban zaɓen shugaban Ƙasa na 2023. Asiwaju mai nasara ne kuma jigo a fagen siyasa wanda ya samu nasara da dama. Yana da duk abubuwan da ya kamata ya kai mu ga nasara da ɗorawa daga ayyukan Shugaba Muhammadu Buhari”Inji Sanata Uba Sani

Bari in yi amfani da wannan dama domin in gode wa kwamitin ayyuka na Ƙasa na jam’iyyar APC, da gwamnoninmu bisa himma wajen gudanar da babban taro na musamman”.

” Godiyata ga mai girma Shugaban Ƙasa don samar da tsarin zaɓe mai kyau wanda ya ba mu damar yin babban taro cikin salama.

Dole mu cigaba da aiki, ba tare da hutawa akan bakanmu har sai an tabbatar da nasara a babban zaɓe mai zuwa na Shekarar 2023. inji shi Sanata Uba sani.

Sanata Uba Sani na daya daga cikin ƴan takarar Gwamnan jam’iyar APC da ake ganin zasu lashe zaben Gwamna cikin sauki duba da yadda ya Sami karɓuwa daga al’umma masu kaɗa ƙuri’a.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy