Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Katsina a NNPP Nura Khalil ya ware Miliyan Hamsin, domin tallafawa Ƴan Gudun Hijira

0

Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Katsina a NNPP Nura Khalil ya ware Miliyan Hamsin, domin tallafawa Ƴan Gudun Hijira - Dimokuradiyya

Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Katsina a NNPP Nura Khalil ya ware Miliyan Hamsin, domin tallafawa Ƴan Gudun Hijira

Kamar yadda aka sani Injiniya Nura khalil ya kafa wata Gidauniya mai suna Nura Khalil Foundation wadda mai dakin sa Hajiya Farida Barau take jagoranta.

Ita wannan Gidauniyar tafi ƙarfin shekara goma (10) da kafata, inda wannan Gidauniyar ta kasance kullum aikin ta taimakon Marayu da ƴan gudun Hijra, taimakawa matasa maza da mata wajen karatun su.

Ganin yadda ƴan gudun Hijra ke ta shan wahalhalu, babu wajen kwana babu wajen zama, ga yunwa ta masu katutu sai sun fita sunyi barar abunda zasu ci da su da ɗiyan su,

Haka zalika wasu kan faɗi cewa sai anyi fasikanci da su ake basu abunda zasu kai ma iyalan su subhanallahi! A dalilin hakan ne yasa Engr Nura khalil ya ware Miliyan Hamsin (50,000,000) domin ganin sun wadatu da abinci da tufafi.

A zantawar da shi yace idan har mutum zai iya mika kuɗin sa ya siya form ɗin takara to shi a nashi tunanin gara ya taimaka ma waɗannan bayin Allah da iftila’i ya fada mawa, kana ji kana gani a raba ka da gidan ka, wasu an kashe su, wasu kuma an sace su har yau babu labarin su

A ƙarshe ya ƙara da cewa yana jajantama al’ummar jahar katsina ga baki ɗayan su akan fargaba da har kullum suke kwana suke tashi da shi a zukatan su.

Da haka ne yake bada shawarar kowa ya dukufa addu’a ba dare babu rana har Allah ya kawo ma jahar katsina sauki Ameen.

#NNPP2023

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy