2023: APC Zata iya shan kaye idan ta baiwa Ɗan Arewa Takara — Inji Akeredolu

0

2023: APC Zata iya shan kaye idan ta baiwa Ɗan Arewa Takara — Inji Akeredolu - Dimokuradiyya

2023: APC Zata iya shan kaye idan ta baiwa Ɗan Arewa Takara — Inji Akeredolu

Gwamnan Jahar Ondo Oluwarotimi Akeredolu SAN ya gargaɗi Jam’iyyar APC akan bada tikitin tsayawa takarar ga Ɗan Arewa.

A cikin wani rubutu daya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Alhamis, Akeredolu wanda shine Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, yayi kira ga Jam’iyyar data yi aiki tuƙuru wajen cigaba da mulki ta hanyar miƙa shi ga Yankin Kudu.

The PUNCH ta bada rahoton cewa an samu rabuwar kai akan miƙa Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023.

“Dole Jam’iyyar APC tayi aiki tuƙuru domin ta cigaba da mulki. Dole mu miƙa mulki ga yankin Kudu…. Shikenan ,” Inji shi.

Baya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa da Tsohon Gwamnan Jahar Lagos, Bola Tinubu, Sauran ƴan Takarar APC sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan da Tsohon Ministoci Rotimi Amaechi, da Ogbonnaya Onu, da Godswill Akpabio da Chukwuemeka Nwajiuba.

Gwamnonin dake neman Takarar sune Kayode Fayemi (Ekiti) da Yahaya Bello (Kogi), da Dave Umahi (Ebonyi) da Ben Ayade (Cross River) da Badaru Abubakar (Jigawa).

Sauran sun haɗa da Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Ken Nnamani, Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, da Sanatoci Ibikunle Amosun, da Ajayi Boroffice, da Rochas Okorocha.

Abokin Takarar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Shekarar 2011, Fasto Tunde Bakare, da Uju Ken-Ohanenye, da Nicholas Felix, da Ahmad Rufa’i Sani, sa Tein Jack-Rich, da Ikeobasi Mokelu suma duk suna cikin ƴan Takarar Shugaban Ƙasa.

Akeredolu a watan mayu ya gargaɗi APC akan miƙa tikitin ta na Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023 zuwa yankin Arewa, yana cewa hakan zai haifar da rikici.

A cewar sa, yanzu lokaci ne da yankin Kudu na Kasar nan suma su fito da shugaban kasa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy