2023: Dalilin Daya Sa Masu Neman Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa 10 Basu Can Canta Ba Bayan Tantance Su – APC

0

2023: Dalilin Daya Sa Masu Neman Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa 10 Basu Can Canta Ba Bayan Tantance Su – APC - Dimokuradiyya

John Oyegun, shugaban kwamitin tantancewa na jam’iyyar APC, ya bayyana dalilan da suka sa wasu masu neman tsayawa takarar shugaban kasa basu can canta ba a ranar Juma’a.

Akalla maza 10 da ke neman tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam’iyya mai mulki aka yanke sunayen su.

Da yake gabatar da rahoto ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, Oyegun ya ce: “Batun da nake so in yi shi ne ingancin mutanen da ke son mulkin kasar nan.

“Mu jam’iyya ce mai mulki don haka ikon shugabanci, asali, gogewa … a kan tushen da muka sanya jerin sunayen.

“Ba zan so in karanta sunayen ba, zan bar muku wannan, amma mun kawo adadin lambar sunaye 13.

“Za mu iya yanke shi ɗan guntu amma muna son ƙaramin abubuwa su bayyana.”

Har yanzu dai ba a san cikakken bayani kan masu neman shugabancin kasar da ba su can canta kan yanke wannan shawara ba.

Jam’iyyar PDP a Jahar Ogun tayi kira ga Fusatattun Ƴan Takarar Gwamna guda biyu dasu je Kotu tare da neman haƙƙin su, idan basu gamsu da sakamakon Zaben Fidda Gwani da aka gabatar a ƴan kwanakin nan.

Dayake jawabi ga Manema labaru a Sakatariyar Jam’iyar dake Abeokuta, Babban Birnin Jahar Ogun, Shugaban Jam’iyyar Sikirulahi Ogundele yayi kira ga ƴan Takara Segun Showunmi da Jimi dasu sanya Jam’iyyar a cikin zuciyar su.

Ogundele ya ayyana Fusatattun Ƴan Takarar dake cewa sun samu nasara a matsayin masu neman tada zaune tsaye.

Yace Dan Takarar da aka zaba a PDP a Jahar Ogun shine Oladipupo Adebutu, kuma babu wani sai shi.

Showunmi a ranar 25 aka gudanar da zaɓen fidda Gwani inda aka zaɓe shi a matsayin Ɗan Takarar Gwamna.

Lawal, wanda ya jagoranci Zaben Fidda Gwani daya fitar da Adebutu a matsayin Ɗan Takarar, yayi kira da aka soke zaben a Jahar, yana mai cewa sunayen Deliget da aka yi amfani dasu wajen zaɓen bana gaskiya bane.

Amma Jam’iyyar PDP tace bata yi wani zaɓen fidda Gwani guda a ko’ina.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy