- Advertisement -

2023: Kwanaki 3 ga ƙarewar wa’adi, har yanzu NNPP, AAC basu tura sunan ko Mutum 1 ga INEC

0

2023: Kwanaki 3 ga ƙarewar wa’adi, har yanzu NNPP, AAC basu tura sunan ko Mutum 1 ga INEC - Dimokuradiyya

2023: Kwanaki 3 ga ƙarewar wa’adi, har yanzu NNPP, AAC basu tura sunan ko Mutum 1 ga INEC

- Advertisement -

Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta INEC tace Jam’iyyun siyasa guda biyu AAC da NNPP har yanzu basu ɗora sunan ko mutum ɗaya ga Ƴan Takarar Gwamnan da Mataimakan su a shafin Ƴan Takarar da INEC ta bayar ICNP.

Kwamishinan Hukumar kuma Shugaban Kwamitin Kula da Bayanai da Ilmantar da Masu Kaɗa Ƙuria Festus Okoye ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin wata sanarwa.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu.

- Advertisement -

A cewar sa, kamar yadda aka bada a jadawalin gudanar da harkokin zaɓe na INEC da aikace-aikacen Babban Zaɓen Shekarar 2023 da Hukumar ta fitar a ranar 26 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022, dukkanin Jam’iyyun siyasa da suka gudanar da Sahihin zaɓe su tura sunayen Gwamnoni da Mataimakan su da na Ƴan Majalisu a shafin Hukumar na ICNP daga 1 ga wata zuwa 1t ga watan Juli na Shekarar 2022.

Yace ” a halin yanzu ta samu bayanai sunayen mutane dubu 6,995 da aka ɗora daga jam’iyyu 16 daga cikin 18 daga Mazaɓun da suka gabatar da ƴan Takarar su.

“Amma Jam’iyyu guda biyu, AAC da NNPP basu ɗora koda sunan mutun guda ba. Hukumar tana tunatar da dukkanin Jam’iyyun Siyasa cewa suna da kwanaki uku su ɗora sunayen ƴan Takarar su ga ICNP.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy