2023: Sultan, Tambuwal Sun yi kira ga Maniyyata Aikin Hajji dasu yi addu’ar samun Shuwagabanni Nagari

0

2023: Sultan, Tambuwal Sun yi kira ga Maniyyata Aikin Hajji dasu yi addu’ar samun Shuwagabanni Nagari - Dimokuradiyya

2023: Sultan, Tambuwal Sun yi kira ga Maniyyata Aikin Hajji dasu yi addu’ar samun Shuwagabanni Nagari

Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa’ad Abubakar da Gwamnan Jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal sun kira ga ƴan Najeriya da zasu halarci Hajjin wannan Shekarar dasu addu’ar samun Shuwagabanni Nagari a Babban zaɓen Shekarar 2023.

Sun yi wannan kiran ne a Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar dake Sokoto, a lokacin da suke ƙaddamar da Jirgi na farko daya ɗauki Maniyyata Aikin Hajji 420 daga Jahar zuwa Ƙasa mai tsarki ta Makka dake Ƙasar Saudiyya a daren ranar Lahadi.


Download Mp3

Sultan yayi kira ga Maniyyata Aikin Hajji dasu Addu’ar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma zaɓe na adalci, gami da yin kira a garesu dasu yi addu’ar samun Shuwagabanni Nagari a dukkanin matakai.

Gwamnan a jawabin sa, ya buƙaci Maniyyata Aikin Hajji dasu Addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai, da cigaba a Jahar, dama ƙasa baki ɗaya.

Ya bukace su dasu kasance masu yin biyayya ga Dokokin Hajji, gami dana cutar Covid-19, yana mai cewa Gwamnati tayi dukkanin abinda ya dace domin samun nasarar shirin.

Shima a nashi Jawabin, Shugaban tawagar daga Gwamnati, kuma Majalisar Dokokin Jahar Aminu Manya Achida ya bada tabbacin kwamitin shi na jajircewa domin samun nasarar shirin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy