Abba Gida-Gida Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam’iyyar NNPP

0

Abba Gida-Gida Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam’iyyar NNPP - Dimokuradiyya

Alhaji Abba Kabir-Yusuf ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano.

Duk da cewa a baya Kabir-Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba Gida-Gida” ya fito ba tare da hamayya ba, amma wakilai 1,452 ne suka tabbatar da takararsa a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa Sanata Musa Bako daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa ne ya sa ido a kan tabbatar da hakan.

Bako ya bayyana cewa wannan tabbaci ya zama dole, duk da cewa Kabir-Yusuf ne kawai dan takarar gwamna a jam’iyyar.


Download Mp3

“Wakilai uku daga kowane yanki 484 sun tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023,” in ji shi.

Jim kadan bayan tabbatar da hakan, Kabir-Yusuf ya godewa ‘yan jam’iyyar, wakilai da sauran masu ruwa da tsaki da suka ba shi wannan mukami.

Ya kuma yi kira ga ’yan uwa da su yi aiki tukuru da ci gaba da kasancewa tare domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

(NAN)

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy