- Advertisement -

Abinda Tinubu ke fama dashi a halin yanzu kan zaɓar Mataimaki a Takarar sa — Akeredolu

0

Abinda Tinubu ke fama dashi a halin yanzu kan zaɓar Mataimaki a Takarar sa — Akeredolu - Dimokuradiyya

Abinda Tinubu ke fama dashi a halin yanzu kan zaɓar Mataimaki a Takarar sa — Akeredolu

- Advertisement -

Gwamnan Jahar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya bayyana abinda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke fama dashi akan samun wanda zai yi mashi Mataimaki a Babban Zaɓen Shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana cewar akwai abubuwa da dama da za’a lura dashi wajen zaɓen abokin Takarar Tinubu, wanda ya sanya da wahala ga Tsohon Gwamnan Jahar Lagos.

Ba tare da bayyana Addini wanda shine abinda ƴan Najeriya ke ta mahawara akan shi, Gwamna Akeredolu ya bayyana muhawarar sa akan Shiyya, biyayya da kuma yankin da keda ƙuri’u masu yawa, wanda sune suka cazawa Ɗan Takarar kai akan wanda zai zaɓa yayi mashi Mataimaki a Takara.

- Advertisement -

Da yake bayyana a shirin gidan Talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu a Yau a ranar Litinin da yamma, Gwamnan ya bayyana cewa “abubuwan da Asiwaju Bola Tinubu ya tsinci kan sa, shine abinda nake cewa sai anyi ƴar Canje. Misali kaga bazai zaɓa daga yankin Kudu ba. To kaga an barshi ya zaɓa a yankin Arewa.

“Saboda shi daga Kudu yake, bazai zaɓa daga yankin Kudu maso Gabas ko kuma Kudu maso Kudu, saboda daga yankin Kudu maso Yamma yake, dole ne ya zaɓo daga yankin Arewa.

“Idan ka duba a Arewa, akwai abubuwa da dama da zaka duba. Wasu zasu ce ka zaɓo daga yankin Arewa maso Yamma, wannan shine inda Shugaban Ƙasa ya fito.

- Advertisement -

“Wasu kuma zasu ce to ka zaɓo daga Yankin Arewa maso Gabas, shima abin dubawa ne.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy