- Advertisement -

Abokin Takara: Wasu Jiga-Jigai a APC, sun buƙaci Kotu ta hana Tinubu canja Kabir Masari

0

Abokin Takara: Wasu Jiga-Jigai a APC, sun buƙaci Kotu ta hana Tinubu canja Kabir Masari - Dimokuradiyya

Abokin Takara: Wasu Jiga-Jigai a APC, sun buƙaci Kotu ta hana canja Masari

- Advertisement -

An buƙaci Babbar Kotun Tarayya ta Abuja data hana Jam’iyyar APC daga musanya Alhaji Kabiru Masari a matsayin abokin takarar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Bayan Tinubu ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, ya mika sunan Masari ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC a matsayin wanda zai riƙe ofishin kafin samo wanda ya cancanta.

Amma wasu Jiga-Jigai a Jam’iyyar APC Wanda Suka kasance Deliget ne a Zaben Jam’iyyar na Shugaban Ƙasa, Zakari Maigari, da Zubainatu Mohammed sun je Kotu domin ta hana INEC daga amsar canja suna Mataimaki a Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, baya ga Masari.

- Advertisement -

Jam’iyyar APC, Tinubu, da Kabiru Masari sun kasance a matsayin wanda ake ƙarar a wata Shari’a mai lamba ta FHC/ABJ CS/1059/2022, Mai Kwanan watan r ga watan Juli na Shekarar 2022.

Wanda suke shigar da ƙara ta hanyar lauyan su Hakeem Kareem, suna so Kotu ta duba sashe na 142(1) d sashe na 29(1), 31, da 33 na Dokar Zaɓe, a Shari’an ce za’a iya korar abokin Takara, ko kuma canja shi da wani domin tunkarar Babban Zaɓe na Shekarar 2023.

Daga abinda suke so shine Kotu ta duba yiwuwar abinda tikiti ya bada na sashe 142(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, ya nuna cewa baza’a iya kai tsaye a kori Ɗan Takarar a Shugaban Ƙasa, idan aka duba Babban Zaɓen Shekarar 2003.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy