- Advertisement -

Abubuwa 3 Da Za A Rika Tunawa Da Daraktan ‘Izzar So’ Nura Mustapha Waye

0

Abubuwa 3 Da Za A Rika Tunawa Da Daraktan ‘Izzar So’ Nura Mustapha Waye

A karshen makon da ya gabata ne Allah ya yi wa Daraktan fim mai dogon zango na “Izzar So” Nura Mustapha Waye rasuwa.

- Advertisement -

Jarumin fim din na “Izzar So” Lawan Ahmad ne ya bayyana rasuwar Nura a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi Aminiya ta rawaito.

Nura Mustapha, darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana’antar ta Kannywood.

Fim din na Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya.

- Advertisement -

Kiyasi da aka yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa fim din shi ne ya fi yawan masu kallo a dandalin YouTube da ake nuna fim din.

A wata hira da Aminiya ta yi da Balarabe Tela, wani dan uwa ga marigayin kuma tsohon jarumi a Kannywood, ta samu jin wasu abubuwa guda 3 da za a rika tunawa dangane da marigayi Nura Mustapha Waye.

Ya dade a masana’antar shirya fina-fanai ta KANNYWOOD:

- Advertisement -

Izzar So ba shine fin na farko ba na Marigayi Nura Mustapha ba. Marigayin ya dade da shiga masana’antar ta Kannywood tun shekarar 2001. Ya kuma yi fina-finai da dama.

Lakabin WAYE a sunansa

Ana yi wa marigayin lakabi da WAYE ne saboda da shi ne fim dinsa farko, wanda a bisa al’adar ‘yan masana’antar ana yi wa mutum lakabi da wani fim da ya fara yi, ko kuma ya yi suna a cikinsa.

- Advertisement -

Ilimin addini da kuma mu’amalla ta gari

Marigayi Nura makarancin Al kura’ni ne da kuma littafina yabo na manzon Allah (SAW) Dala’ilu khairat.

A cewar Balarabe Tela, “ko a ranar da zai rasu sai da ya yi karatunsa na Qur’ani da Dala’ilu kamar yadda ya saba a kullum.

- Advertisement -

“Sakamakon ilimin addini da ya taso da shi Hakan kuma ya tasirantu matuka a fim dinsa na Izzar So.”

Balarabe ya kuma ce, marigayin ya na da mu’amala mai kyau da jama’a, ba wai a Kannywood ba, hatta a unguwarsu ta Goron Dutse mutane sun ji rasuwarsa sosai soboda kyakyakyawar mu’amallarsa.

Nura Mustapha ya arasu ne a ranar Lahadi da safe, tuni aka yi jana’izzarsa a unguwarsu ta Goron Dutse a Kano, kamar yadda musulunci ya tanada.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy