- Advertisement -

Abuja-Kaduna: Iyalan Sauran Matafiya 51 dake hannun Ƴan bindiga, sun yi gargaɗin karɓe wasu Ma’aikatun Gwamnati

0

Abuja-Kaduna: Iyalan Sauran Matafiya 51 dake hannun Ƴan bindiga, sun yi gargaɗin karɓe wasu Ma’aikatun Gwamnati - Dimokuradiyya

Abuja-Kaduna: Iyalan Sauran Matafiya 51 dake hannun Ƴan bindiga, sun yi gargaɗin karɓe wasu Ma’aikatun Gwamnati

- Advertisement -

Iyalan sauran mutane 51 wadanda aka sace ƴan uwan su a harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna a ranar Juma’a sun yi gargaɗin ƙwace manyan Ma’aikatun Gwamnati a Kaduna da Abuja, sakamakon kasawar Gwamnati na ceto ƴan uwan su.

Ƴan bindiga sun yi gargaɗin kashe waɗanda ke hannun su, idan har Gwamnati bata biya su abubuwan da suka buƙata ba.

Kwanaki kaɗan da suka gabata, sun harbe mutum guda, suna tura wani saƙo ga Gwamnati cewa kashe su bazai yi masu wahala ba.

- Advertisement -

Biyo bayan wannan, iyalai da Abokanai na sauran waɗanda ƴan uwan su ke hannun ƴan bindiga, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun su Dr. Abdul’aziz Atta, ya bayyana tsoro na rasa iyalan su, musamman da rahoton nin da yazo na ci zon Macizai, da raunuka, wanda suke cigaba da shan wahala.

Atta, Wanda Mahaifiyar sa da Ƴar uwar sa sun a hannun su, ya bayyana damuwa akan yanda lafiyar su take a hannun su.

A cewar sa “kamar yadda take shine babu wani magani, babu wanda ya cire harsashi daga jikin su, kawai kayi tunanin yanda halin mutum zai kasance a Daji.

- Advertisement -

Yace duk da Gwamnati ta yi wani yunkuri, wanda 11 daga cikin ƴan uwan su aka sako su, amma dole sai ta ƙara sauri wajen ceto sauran mutanen da suka sace.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy