Adamu Garba Ya fice Daga Sahun Yan Takarar Shugaban Kasa

0

Adamu Garba Ya fice Daga Sahun Yan Takarar Shugaban Kasa - Dimokuradiyya

Wani tsohon jigo a jam’iyyar APC, wanda kuma ya yi watsi da jam’iyyar saboda tsadar fom na bayyana sha’awa da tsayawa takara, Adamu Garba, ya dakatar da takararsa na shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Adamu bayan ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar Young Progressives Party inda ya mallaki fom din sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa.

Sai dai ya sanar da dakatar da takararsa na shugaban kasa a yau Talata.


Download Mp3

Adamu ya ce, “’Yan uwa, bisa ga burina na tsayawa takarar Shugabancin Tarayyar Najeriya a zaben 2023 mai zuwa, mun gano wasu muhimman abubuwa wadanda a halin yanzu suka ci karo da muradinmu da kuma burinmu na kawo sauyi mai kyau domin samun canji mai kyau, fagen siyasar Najeriya.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kara da cewa zai ba da fifiko ga muradun matasan Najeriya.

Ya ce, “Ga daukacin Matasan Nijeriya; Namiji ko mace; Dole ne dukkanmu mu yi aiki tare don kai Najeriya zuwa mataki mafi girma.

“Bai kamata mu ja da baya ba, kada mu yi taurin kai, kada mu karaya,” inji dam takarar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy