Alamu sun nuna jam’iyyar PDP a zaben Ekiti cewa……..

0

Alamu sun nuna jam’iyyar PDP a zaben Ekiti cewa…….. - Dimokuradiyya

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Ekiti ba lallai ta iya tabuka wani abin azo a gani a zaben gwamnan da ake yi a yau ba.

Hakan dai na da nasaba da karancin kudade daga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta fuskar sakin su yadda ya kamata.

Baya ga rashin kudi, wasu mazauna garin Ado-Ekiti, babban birnin jihar, sun ce fadan da ake yi a zaben na yau yana tsakanin jam’iyyar APC da SDP.


Download Mp3

Mista Olufemi, wani mazaunin garin ne ya ce: “An gama PDP a jihar Ekiti. Ko dai APC ko SDP ka san mutane suna jin yunwa bukatar sauyi.”

Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa Kola, ya ce zai yanke shawarar wanda zai zaba idan ya isa rumfar zabe.

An tattaro cewa soke babban gangamin karshe na jam’iyyar PDP ya yi babbar illa ga dan takarar jam’iyyar, Bisi Kolawole.

Wani dan jam’iyyar PDP na Ekiti da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da gwamna Nyesom Wike ya fadi shi ne ke da alhakin makomar jam’iyyar a Ekiti.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy