Allah Yayiwa Momin Uwar Mashahurin Jarumin Rasuwa Ga Cikakken Labari Nan Kasa:- 

INNA lillahi wa inna ilahair raji’un! A ranar Asabar, 5 ga Satumba, 2020, Allah ya yi wa kakar fitaccen jarumi kuma furodusa, mazaunin Zariya, Aminu Ahmad (Mirror), rasuwa.

Marigayiyar, Malama Hannatu Yahaya (Umma Maiwaina), ta rasu ne a gidan ta da ke Layin Mai’unguwa, a Unguwar Dosa, Kaduna. 

Malama Hannatu, mai kimanin shekara 86, ta rasu ne bayan ta sha fama da rashin lafiya. 

Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar, namiji ɗaya, mata huɗu. Kuma kakar Aminu Mirror ce ta wurin mahaifiya.

Da fatan Allah ya jiƙan ta, ya sa Aljannar Firdausi ce makoma, amin.

Munah Baran Addu’ar Ku,

Ku Tura Zuwa Wasu Groups Da Facebook WhatsApp Twitter Instagram.

Ku Kasance Tare Damu A Wannan Shafin Domin Samun Sabbin Labaran Kannywood Da Wakokin Siyasa Dana Hausa.