- Advertisement -

Amaechi ya isa Rivers, yasha alwashin samun nasarar APC a 2023

0

Amaechi ya isa Rivers, yasha alwashin samun nasarar APC a 2023 - Dimokuradiyya

Amaechi ya isa Rivers, yasha alwashin samun nasarar APC a 2023.

- Advertisement -

Tsohon Ministan Sufuri na Nijeriya Rotimi Amaechi yace ya dawo Jihar Rivers domin tabbatar da samun nasarar Jam’iyyar APC a Babban Zaɓen Shekarar 2023.

Amaechi ya bayyana haka jim kaɗan bayan ya isa Filin Jirgin Saman Port Harcourt, Omagwa a ranar Asabar.

Ya samu tarba daga Shuwagabannin Jam’iyyar APC, da ɗumbin magoya bayan sa.

- Advertisement -

Tsohon Ministan yasha alwashin magance dukkanin matsalolin dake cikin Jam’iyyar wanda ya sanya ya faɗi a Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC da aka gudanar a watan daya gabata.

Ya yi kira ga ɗumbin magoya bayan Jam’iyyar dasu mara masa baya domin cimma nasara.

Da yake jawabi akan zargin rashin dai-dai a zaɓukan Fidda Gwani a Jihar, Amaechi ya bayyana masu wannan maganar a matsayin wanda ke Son Maimaita abunda ya faru a 2019 a jihar.

- Advertisement -

Ya bada tabbacin cewa Jam’iyyar APC Zata kasance a nasara a shekara mai zuwa.

Yace “duk wanda ke tsoron zaɓe kuma suna Son zuwa Kotu su cire sunayen mutane daga takardar, na ɗauka sun yi suna?

“Zamu jaraba sunan mu, mu gani a zaɓe. Mun amince da Kotu, adalci za’a yi shi. Abun mu shine aiki. Shiyasa nazo.

- Advertisement -

Amaechi shine yazo na uku a zaɓukan Fidda Gwani a watan daya gabata da ƙuri’u 316.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy