An raɗa wa ɗan Fati Ladan suna

0

An raɗa wa ɗan Fati Ladan suna

Yerima Shettima rungume da ɗan sa Amir

A YAU Litinin, 18 ga Afrilu, 2022 aka raɗa wa ɗan da tsohuwar jaruma Fati Ladan ta haifa a makon da ya gabata.

An raɗa wa jaririn suna Muhammad Shafi’u, amma za a riƙa kiran sa da Amir.

Mijin Fatin, wato Alh. Yerima Shettima, ya shaida wa wakilin mujallar Fim cewa sunan mahaifin sa ne aka raɗa wa jaririn.


Download Mp3

Yerima da Fati

An yi raɗin sunan ne a Gidan Bugu, cikin garin Zariya, Jihar Kaduna.

Sai dai kuma ba yi taron suna ba sai bayan Sallah idan Allah ya kai mu da rai da lafiya.

Idan ba ku manta ba, a ranar Litinin da ta gabata mun ba ku labarin haihuwar da Fati Ladan ta yi da misalin ƙarfe 8:17 na safe, a wani asibitin kuɗi da ke Unguwar Rimi, Kaduna.

Allah ya raya Amir, ya albarkaci rasuwar sa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy