An zaɓi Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kano, tare da rantsar da shi

0

An zaɓi Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kano, tare da rantsar da shi - Dimokuradiyya

Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi Hon. Kabiru Hassan Dashi a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin ta jihar Kano.

Hon. Dashi ya kasance dan majalisa mai wakiltar al’ummar karamar hukumar Kiru dake jihar Kano.

Majalisar ta zabe shine yayin zamanta na yau Litinin, wanda ya gudana bisa jagorancin shugaban ta Hamisu Ibrahim Chidari.


Download Mp3

Zaben nasa ya biyo bayan ajiye mukamin da tsohon mataimakin shugaban majalisar Hon. Zubairu Hamza Massu yayi wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP daga APC.

Kabiru Dashi, ya karbi rantsuwa a wajen daraktan shari’a na majalisar Nasidi Aliyu yayin zaman majalisar na yau.

Haka zalika yayin zaman shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta takardar dan majalisar jiha mai wakiltar Bebeji Abubakar Uba Galadima, shima dake bayyana ficewar sa daga jam’iyar APC zuwa NNPP.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy