- Advertisement -

Ana Zargin Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Gyaran Hali na Kuje Dake Abuja

0

Ana Zargin Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Gyaran Hali na Kuje Dake Abuja - Dimokuradiyya

A daren Talatar nan an jiyo karar fashewar wani abu kusa da gidan Yarin Kuje, dake babban birnin tarayya Abuja, kuma daga bisani kuma sai harbe harbe bindiga.

- Advertisement -

To sai dai har kawo lokacin haɗa wannan rahoto babu labarin ainihin abinda ke faruwa a wajen.

Kuma an kasa samun wani jami’in gidan da zai yi karin haske kan abinda ke faruwa.

Duk kokarin jin karin haske daga bakin mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya Umar Abubakar, hakan ya gaza tabbata.

- Advertisement -

Mazauna yankin sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren Talatar nan.

Wasu daga cikin makusantan gidan sun ce zargin da suke ba zai wuce harin yan bindiga ba, wanda suka kai don cimma wata manufa tasu.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy