APC: Dalilan da suka sanya har yanzu Tinubu bai Ziyarci Ƙungiyoyin Yarbawa, Inyamurai — Hadimin sa

0

APC: Dalilan da suka sanya har yanzu Tinubu bai Ziyarci Ƙungiyoyin Yarbawa, Inyamurai — Hadimin sa - Dimokuradiyya

APC: Dalilan da suka sanya har yanzu Tinubu bai Ziyarci Ƙungiyoyin Yarbawa, Inyamurai — Hadimin sa

Hadimin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC na ɓangaren Kafafen Yaɗa Labaru Bola Ahmed Tinubu, kuma Jigo a Jam’iyyar, Seye Oladejo ya bayyana dalilan da suka sanya har yanzu sabon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa har yanzu bai ziyarci Ƙungiyoyin Yarbawa da Inyamurai bayan ya samu nasarar Lashe Zaɓen Fidda Gwani.

Gwamna karo na biyu na Jahar Lagos, a ranar Laraba data gabata ya lashe zaben fidda gwani na shugaban ƙasa a Jam’iyyar APC domin tunkarar Zaɓen Shekarar 2023, bayan ya samu ƙuri’u 1, 271 a Zaɓen da aka gudanar, inda ya kada ƴan Takara 13 domin samun Tikitin Tsayawa Takarar a Zaɓen Jam’iyyar daya wakan a filin taro na Eagles Square dake Abuja.


Download Mp3

A wani ƙokari da yayi bayan ayyana shi a matsayin Wanda ya lashe Zaɓen, Tinubu ya ziyarci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo abokin takarar sa, da sauran ƴan Takarar da Ƙungiyoyi a Abuja.

A lokacin da aka tuntuɓe shi akan yaushe ne Tinubu, zai gana da Ƙungiyoyin Yarabawa da Inyamurai, Ramon ya maida jawabi “nan bada jimawa Asiwaju zai gaba da Ƙungiyoyin.”

Oladejo a jawabin sa yace “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Dan Takarar Shugaban Ƙasa yana shirin ganawa dasu domin gudun wani matsala.

Oladejo ya kuma yi jawabi akan zargin da Lauyan Najeriya Ebun-Olu Adegboruwa cewa Gwamnan Jahar Lagos ta ƙyale mulki ya koma yaƙin neman zaɓen Asiwaju Bola Tinubu.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy