APC: Dalilin Da Yasa Gwamna Yahaya Bello Ya Ki Ganawa Da Buhari Saboda Bai Yarda Da Matsayarmu Ba – El-Rufa’i

0

APC: Dalilin Da Yasa Gwamna Yahaya Bello Ya Ki Ganawa Da Buhari Saboda Bai Yarda Da Matsayarmu Ba – El-Rufa’i - Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana dalilan daya sa takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bashi uzuri daga ficewa a taron gwamnonin jam’iyyar APC na arewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan haka, El-Rufai ya bayyana cewa gwamnoni 13 daga cikin 19 na APC daga Arewa sun amince cewa a ware tikitin takarar shugaban kasa na APC zuwa yankin Kudu.

Gwamnan Kaduna, ya yi ikirarin cewa Bello, wanda shi ma dan takarar shugaban kasa ne na APC, ya yanke shawarar kin halartar taron.

“Gwamnan jihar Kogi ya zabi ya ba kansa uzuri daga ganawar da ya yi da shugaban kasa, saboda bai yarda da matsayarmu ba.

“Akwai gwamnonin APC 14 a cikin jihohin Arewa 19. Mu 13 ne a shafi daya kan wannan batu kuma duk mun zo ganin shugaban kasa.


Download Mp3

“Amma gwamnan jihar Kogi ya ba wa kansa uzuri, kuma yana cikin hakkinsa na dimokuradiyya don yin uzuri kansa,” in ji El-Rufai.

Gabanin Babban Zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023, Fitaccen Mawaƙi a Najeriya Peter Okoye da akafi sani da Mr P, ya bayyana cewa zai daina karɓar duk wani wanda bai da Katin Zaɓe daga Ziyartar sa.

Mr P, daya daga cikin tagwaye na P Square ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a shafin sa na Twitter a ranar Litinin.

Mawaƙin yace baiwa Jami’an tsaron sa umarni da kada su bar kowa yazo wurin sa, ba tare da katin zaɓe na Din-Din-Din.

“Yanzu na baiwa Jami’an tsaro na umarni cewa kada wanda aka bari ya ziyarce ni gidana ko ofishina ba tare da ya nuna PVC na shi ba.”

“Har da Shuwagabanci na da tawaga ta cewa babu Kati! Babu ziyara! Dole mu kori Shuwagabannin mu ruɓaɓɓu. Ya rubuta a Twitter.

Za’a fara Zaɓen Shugaban Ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairu na Shekarar 2023. Tun 2019, kimanin mutane miliyan 20 ƴan Najeriya suka zamanto suna da Shekaru 18, kuma zasu iya zaɓe.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy