APC; Mutum Guda Cikin Yan Takarar Shugaban Kasa, Yaki Amincewa Da Masalahar Cikin Gida

0

APC; Mutum Guda Cikin Yan Takarar Shugaban Kasa, Yaki Amincewa Da Masalahar Cikin Gida - Dimokuradiyya

Shugaban kwamitin tantance yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC John Odigie-Oyegun, ya ce kaso 99% cikin yan takarar shugaban kasa 23 sun amince da zabar guda cikin su domin tsayawa jam’iyyar takara a zabe mai zuwa.

A cewar Ogeyun mutum ɗaya ne cikin takarar yaki amincewa da wannan tsari duk kuwa da cewa bai bayyana sunansa ba.

Odigie-Oyegun ya bayyana haka ne a yayin mika rahoton sa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu a yau Juma’a.

Ya shaidawa jam’iyyar cewa ya kamata ta kara datse jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa 13 da suka yi nasarar tsalle tantancewar kwamitin.


Download Mp3

A yau ne dai kwamitin ya sanar da cire sunayen yan takara 10 cikin 23 da suke son tsayawa jam’iyyar takara, bayan da suka gaza cika sharudan kwamitin.

Duk da dai bai ambaci wanda ya ki amincewa da wannan ra’ayin ba, amma da yawa daga cikin ‘yan siyasa sun yi imanin cewa zai iya kasancewa jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, wanda sansaninsa bai goyi bayan tattaunawar sulhu ba.

Tinubu dai ya tayar da kura ne a ranar Alhamis inda ya yi ikirarin cewa in ba dan shi ba, da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai zama shugaban kasa a 2015 ba.

Ya kuma bayyana irin yanayin da ya kai ga fitowar Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mataimakin shugaban kasa, inda ya ce Buhari ya ba shi tikitin tsayawa takara, amma wasu jiga-jigan sun nuna adawa da shi saboda adawa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy