Ashe Lilin Baba na da Mata Har Da Ɗa kafin ya Auri Ummi Rahab

0

Ashe Lilin Baba na da Mata Har Da Ɗa kafin ya Auri Ummi Rahab

Jarumar Kannywood Ummi Rahab ta zama matar mawaƙi Lilin Baba ta biyu SHI KENAN, alƙawari ya cika. An ɗaura auren fitaccen mawaƙi, furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba) da fitacciyar jaruma Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), a yau Asabar, 18 ga Yuni, 2022.

An ɗaura auren nasu da misalin ƙarfe 11:00 na safe a wani masallaci da ke NEPA Office, daura da gidan Bala Kasa, a Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N200,000. Fitaccen jarumi Ali Nuhu shi ne waliyyin Lilin Baba, wanda ya karɓi auren.

Da ma shi ne wanda ya kai sadakin tun a watannin baya. ‘Yan fim sun yi wa abokan sana’ar tasu kara, domin kuwa kusan duk wani mai ji da kan sa a Kannywood da ya amsa sunan jarumi, furodusa, darakta, mawaƙi da sauran su ya halarci ɗaurin auren. Palace Hotel, Kano, sun yi anko kafin su tafi wurin ɗaurin aure Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa Nazir M. Ahmad da Adam A. Zango, Yakubu Muhammad da Sani Danja ba su halarci ɗaurin auren ba.

Daga nan wurin ɗaurin auren an ɗunguma zuwa wurin cin abinci wato ‘reception’, wanda aka yi a Meena Events Centre da ke Titin Lodge, Nassarawa, Kano. An ci, an sha, an kuma gyatse. Karanta kuma Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (1) Kafin ranar ɗaurin auren an shirya wasan ƙwallon ƙafa a jiya Juma’a, wanda mata da mazan Kannywood da dama su ka halarta. Wani furodusa ya shaida wa wakilin mu cewa lallai an jima ba a yi bikin da ya tara ‘yan Kannywood haka ba. Cincirindon jama’a a wurin ɗaurin auren Lilin Baba da Ummi Rahab.


Download Mp3

A cewar sa, ba komai ba ne ya jawo wa angon haka ba sai “irin zuciyar da ya ke da ita ta taimakon jama’a”. Ya ƙara da cewa, “Lallai ta tabbata Lilin Baba mutumin kirki ne matuƙa.

Don haka wannan kawai ya ishi waɗanda ba su taimakon mutane izina.” Mujallar Fim ta ruwaito cewa Lilin Baba mutum ne mai tattalin iyalin sa, domin duk wani mai mu’amala da shi a industiri, duk kusancin ka da shi ba ka isa ka ce ka ga matar sa ba. Ya na da uwargida, wata ‘yar garin Jos wadda su ke da ɗa ɗaya da ita. Wata majiya ta ce yaron har ya girma, ya na zuwa makaranta. Ummi Rahab dai ita ce matar Lilin Baba ta biyu a yanzu. Duk da kasancewar sa matashi, kuma mai ɗimbin arziki, bai yarda da a yi dina a bikin sa ba kamar yadda ‘yan Kannywood su ka saba yi.

Ummi Rahab dai za ta tare ne a Kaduna, garin da mijin ta ya ke da zama. Wani makusancin sa ya shaida wa mujallar Fim cewa Lilin Baba ya gina wa Ummi gida a jikin gidan da uwargidan sa ta ke, kowacce da get ɗin ta. Kuma duk gidajen nasa ne na kan sa, ba haya ba ne.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy