Labari Da Dume Dumen Daga Jahar Zamfara:-

Dakarun ‘yan sandan Nijeriya sun samu nasarar bin diddigin wasu hatsabiban barayi masu safarar bindigogi da harsashi suna kaiwa jihar Zamfara.

Barayin sune: Musa Adamu ‘dan shekara 31 mutumin garin Fadan-Karshi a jihar Kaduna, sai Ibrahim Salisu ‘dan shekara 35 mutumjn garin Ruwan-Godiya karamar hukumar Faskari jihar Katsina.

Jaruman ‘yan sandan wadanda suka hana idonsu bacci sun kama barayin ne a daidai tsibirin Dutsen Kudaru kan hanyar Kaduna zuwa Jos dauke da harsashin bindiga guda dubu daya da dari shida da ashirin (1620) za su kai wa wani mutumi mai suna Yello wanda ya fi shahara da sunan Janburos dake garin Dansadau jihar Zamfara.

Barayin sun karbo harsashin bindigar ne daga gurin wani mutumi mai suna Ibrahim wanda yake da zama a garin Barikin-Ladi jihar Pilato, a kan hanyar su na tafiya jihar Zamfara da harsashin sai suka fada tarkon kwararrun ‘yan sanda.

Muna rokon Allah Ya karawa ‘yan sandan Nigeria taimako da nasara akan miyagun mutane masu hana al’ummah zaman lafiya. Amin.

Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Saura Social Media Pls..