- Advertisement -

Atiku Ya Nada Abbmdulrasheed Sharada Da Wasu Mutum Biyu Mataimakansa

0

Atiku Ya Nada Abbmdulrasheed Sharada Da Wasu Mutum Biyu Mataimakansa - Dimokuradiyya

Dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya nada karin mataimaka guda uku ga tawagarsa ta kafafen yada labarai.

- Advertisement -

Mista Abubakar, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya bayyana sunayen mutane uku da aka nada kamar su Abdulrasheed Shehu Sharada, Eta Uso da Demola Olanrewaju, inda ya kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.

A cewar Mista Ibe, “Abdulrasheed, kwararre kan harkokin yada labarai wanda ya kware sosai – wanda ya kwashe shekaru goma yana aiki a kamfanonin yada labarai daban-daban, an nada shi mataimaki na musamman, kan Watsa Labarai.

Ya kara da cewa “Ya kammala karatun Mass Communications daga ISM Adonai, Jamhuriyar Benin kuma Masters a International Relations and Diplomacy, a jami’ar Maryam Abacha American University da Masters akan Journalism and Broadcasting a Girne American University, Cyprus,” ya kara da cewa.

- Advertisement -

An nada Mista Uso, a matsayin Mataimakin na Musamman na Watsa Labarai na zamani, kan ayyuka ga tsohon mataimakin shugaban kasa.

Mista Uso tsohon dalibi ne na Makarantar Gwamnati ta Harvard Kennedy, kuma kwararre ne a Burtaniya da ya horar da Advanced Computing da kwararewa kan tsarin Intanet daga Jami’ar Wales, Bangor.

Shi mamba ne a Cibiyar Injiniya da Lantarki ta Injiniyoyin Kwamfuta, a Burtaniya, da Najeriya.

- Advertisement -

Mista Ibe ya kuma sanya Mista Olanrewaju a matsayin Mataimaki na Musamman na Kafafen Yada Labarai.

Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mista Olanrewaju kwararre ne kan dabarun sadarwa da hulda da jama’a da tarihin Najeriya da akidun siyasa, wanda ya bunkasa a zamaninsa na Shugaban kungiyar dalibai a Jami’ar Ado Ekiti.

“Yana da hannu a cikin farawar kasuwanci da dama kuma ya kawo ilimin masana’antar watsa labaru, haɗin gwiwar kafofin watsa labaru na zamani da ƙwarewar rubuce-rubuce don tsara ra’ayi, labarun fasaha da saƙo ga mutane, kasuwanci da kungiyoyi,” in ji Mista Ibe.

- Advertisement -

(NAN)

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy