Atiku Ya Taya Tinubu Murna, Tare Da Bukatar Ya Zage Damtsen Domin Karawa da Shi

0

Atiku Ya Taya Tinubu Murna, Tare Da Bukatar Ya Zage Damtsen Domin Karawa da Shi - Dimokuradiyya

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yabawa Bola Tinubu tare da taya shi murna bisa nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

Mista Abubakar, dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya ce nasarar da Mista Tinubu ya samu na nuna jajircewarsa.

“Ina taya ku, @officialABAT, kan fitowar ku a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ku. Ina bukatar ka tsage damtse domin karawa dani, amma ka yi nasara ya tabbatar da jajircewarka.” Inji Abubakar a wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Twitter.

Mista Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a ranar Laraba, inda ya samu kuri’u 1,271 inda ya doke abokin karawar sa Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri’u 316 yayin da Yemi Osinbajo, ya samu kuri’u 235.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya zo na hudu da kuri’u 152 a taron da aka kammala ranar 8 ga watan Yuni a Abuja.

Uwargidan shugaban Najeriya kuma shugabar matan shugannin Afirka (AFLPM), Aisha Buhari, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su inganta zaman lafiya a tsakanin al’ummomin manoma domin tabbatar da isasshen abinci a nahiyar.

Ta yi wannan kiran ne a cikin wani sako da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin jama’a da dabaru, Mista Sani Zorro, ya gabatar a ranar Laraba a yayin wani taron koli na kwanaki biyu kan samar da abinci da aka gudanar a Almaty na Jamhuriyar Kazakhstan.

Kungiyar kula da samar da abinci ta Musulunci (IOFS) ce ta shirya taron da nufin inganta samar da abinci da bunkasa noma, musamman kan rawar da mata za su taka wajen samar da abinci.

Ta kuma jaddada bukatar hada karfi da karfe wajen magance munanan illolin da sauyin yanayi ke haifarwa, musamman yadda ya shafi mata da kananan yara da kuma samar da abinci.

Ta ce dole ne hukumomin da abin ya shafa su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen rikicin tsakanin manoma da makiyaya.

A cewarta, lamarin na barazana ga samar da abinci a mafi yawan al’ummomin da suke noma.

Ta ce gwamnatin Najeriya ta sanya isassun kayan aiki don dakile lamarin da kuma tabbatar da tsaro ga al’ummomin manoma.

“Ana kokarin shawo kan lamarin a mafi yawan yankunan da abin ya shafa a Afirka, daya daga cikin kokarin ya fito ne daga kungiyar agaji.

“Kokarin ofishina da gidauniyata, Aisha Buhari Foundation ta ci gaba da tallafa wa mata, matasa da yara wadanda akasari ke fama da kalubalen da suka shafi muhallinmu.

“Mun kuduri aniyar yin amfani da hanyar sadarwa ta matan shugabannin Afirka don yin tasiri kan koyarwar zaman lafiya da ilimin tsaro a makarantun firamare, sakandare da kuma manyan makarantu na yanki a nahiyar,” in ji ta. (NAN)

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy