Awanni bayan dawo wa daga Spain, Buhari zai shilla zuwa Ghana, Kafin Zaɓen APC

0

Awanni bayan dawo wa daga Spain, Buhari zai shilla zuwa Ghana, Kafin Zaɓen APC - Dimokuradiyya

Awanni bayan dawo wa daga Spain, Buhari zai shilla zuwa Ghana, Kafin Zaɓen APC

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bayan ya dawo daga ziyarar daya kai Ƙasar Spain na tsawon kwanaki 3, yanzu kuma zai shilla zuwa Ƙasar Ghana domin wani taron.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa ya fitar Femi Adesina, yace Buhari zai sake yin tafiya zuwa Ƙasar Waje, amma wannan lokacin Ghana zai je.

“Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Asabar, 4 ga watan yuni zai je Accra Babban Birnin Ghana, domin halartar taron ECOWAS akan halin da Gwamnati take a Mali da sauran wasu sassan yankin.


Download Mp3

“Taron wanda zai gudana a Ɗakin taro na Shugaban Ƙasa dake Accra, da akafi sani da Jubilee House, ana saran za’a sake yin dubi akan juyin Mulki da Sojoji suka yi a Mali, domin ganin ta dawo kan turbar Dimokuraɗiyya.

“Haka zalika Shuwagabannin Ƙasashen zasu yi dubi akan yanayin da Jamhuriyar Burkina Faso da Guinea suke ciki.

“Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, da Mai bada Shawara ta Fuskar Tsari Manjo-Janar Babagana Munguno mai ritaya, da Daraktan Hukumar Leken Asiri Ambasada Ahmed Rufa’i.

“Zai dawo zuwa Abuja a rana guda, bayan kammala taron.

Ziyarar Buhari na zuwa ne bayan Jam’iyyar APC take Son ta fito da Ɗan Takara, gabanin Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa da aka canja zuwa wannan satin.

Buhari baya Ƙasar a lokacin da Jam’iyyar ta canja ranar, biyo bayan ƙarin wa’adi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC ta ƙara.

Zaɓen Fidda Gwanin zai wakana a ranar 6, 7 zuwa 8 na watan Yuni.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy