Ba zamu yarda da Takarar Musulmi da Musulmi, domin zai haifar da mance Kiristoci — Inji wani Bishop

0

Ba zamu yarda da Takarar Musulmi da Musulmi, domin zai haifar da mance Kiristoci — Inji wani Bishop - Dimokuradiyya

Ba zamu yarda da Takarar Musulmi da Musulmi, domin zai haifar da mance Kiristoci — Inji wani Bishop

Janar-Sufirtanda na God Mission International Bishop Paul Nwachukwu yace takarar Musulmi da Musulmi a zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023, kiristoci bazasu taɓa amince wa dashi ba.

Nwachukwu yace manyan Jam’iyyu guda biyu da suka zaɓi musulmi a matsayin Ɗan Takarar su tuna cewa Najeriya ƙasa ce mai Mabambantan ra’ayoyi, da addini.


Download Mp3

Yace zaɓen musulmai a matsayin abokanan takarar su, zai haifar da mance kiristoci kenan.

A cikin wata sanarwa mai taken “ina son ƴan Siyasa su tuna cewa Najeriya ƙasa ce mai Mabambantan ra’ayoyi, kuma a wurin ɗaukar abokanan takarar su, baza’a yarda su ƙara ɗaukar wani musulmi ba.

“Najeriya ta kowa da kowa ne, kuma kowane ɓangare da Addini yana da mahimmanci. Zaɓen musulmi a matsayin abokin Takara, zai haifar da mance kiristoci,” Inji Nwachukwu.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy