Babban Taron APC: Tinubu ya ba Deliget ɗin Ogun $25,000, Adamawa $10,000

0

Babban Taron APC: Tinubu ya ba Deliget ɗin Ogun $25,000, Adamawa $10,000 - Dimokuradiyya

Babban Taron APC: Tinubu ya ba Deliget ɗin Ogun $25,000, Adamawa $10,000

Deliget daga Jahar Ogun sun tabbatar da karɓar Dala dubu $25,000 daga tsohon Gwamnan Jahar Lagos.

Haka zalika, sun tabbatar da ƙin amsar Dala dubu $5,000 daga Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo daya basu domin zaɓar su.

“Da farko mutane sun ce Mataimakin Shugaban Ƙasa yace bashi da kuɗin da zai baiwa Deliget tare da shawartar kowa daya zaɓi wanda yake so”, inji wani Deliget.

“Amma daga baya sun dawo sun ce yaso ya baiwa Deliget ɗin Dala Dubu $5,000 domin su ɗauki nauyin zirga-zirgar su da kuɗin Otel.”


Download Mp3

A Wani Labarin kuma.

Alhaji Isa Baba Buji, daya daga cikin wakilan jihar Jigawa a babban taron jam’iyyar APC na musamman da ke gudana a Abuja ya rasu.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa Buji ya rasu a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

Har zuwa rasuwarsa kwatsam, Buji ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da jihar Jigawa ta kudu.

Rahotanni sun bayyana cewa, ya kwana da safe a ofishin hulda da jama’a na Kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, a lokacin da yake shirin zuwa wurin taron.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa, Bashir Kundu, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, “Tabbas ya rasu da safiyar yau”.

Jami’in hulda da jama’an ya kara da cewa “ya fadi a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti ya rasu kafin a isa asibitin. Da muka isa asibitin, an tabbatar da rasuwarsa.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy