- Advertisement -

Babbar Sallah: Yan sanda Sun Kama Mutum 2 Bisa Zargin Satar Ragon Layya A Ogun

0

Babbar Sallah: Yan sanda Sun Kama Mutum 2 Bisa Zargin Satar Ragon Layya A Ogun - Dimokuradiyya

Kwanaki kadan kafin bikin Eid-il-Kabir na ranar Asabar, ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu mutane biyu bisa zargin satar ragon Sallah na wani Sodiq Abolore.

- Advertisement -

An kama wadanda ake zargin, Adetunji Alagbe da Opeyemi Ogunlokun ne a jiya sakamakon rahoton da Abolore ya gabatar a hedikwatar ‘yan sandan Ogijo.

Abolore ya shaidawa ’yan sanda cewa a lokacin da yake barci a dakinsa da misalin karfe uku na safe, sai ya ji hayaniya da ba a saba gani ba a harabar gidansa, inda ya ce hakan ne ya sa ya leko ta tagar.

Yayin da ya leko, Abolore ya ce ya gano an ciro kofar karfen da ya toshe kofar dakin da ya ajiye ragon Sallah nashi da shi.

- Advertisement -

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ruwaito Abolore na cewa ya fita ne ya gano cewa ragon sa na Sallah da ya saya a kan kudi Naira 120,000 ba ya nan.

Oyeyemi ya bayyana cewa, Abolore ya ci gaba da bayyana cewa, a lokacin da ya zagaya, ya ga wasu mutane uku suna tursasa ragon sa cikin wata mota kirar Mazda, wanda hakan ya sa ya daga kararrawa, sannan aka yi wa ‘yan sanda kiran gaggawa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce an kori mutanen uku amma an kama biyu yayin da daya ya tsere.

- Advertisement -

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, da nufin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

A wani labarin kuma na daban.

NCoS tace Fursunoni 4 sun Hallaka, 16 sun jikkata yayin Harin Ta’addancin Jiya

- Advertisement -

Hukumar kula da Gidajen yari ta Ƙasa, NCoS ta ce fursunoni huɗu na gidan yari na Kuje sun mutu yayin da 879 suka tsere a harin da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja.

Umar ya ce maharan sun kutsa cikin gidan yarin ne da ke Kuje, inda suka yi amfani da gurneti su ka ɓalle babbar kofar shiga da kuma ta katanga.

- Advertisement -

Ya ce an kashe jami’in hukumar tsaron fariren hula ta ƙasa, NSCDC da ke tsaron gidan yarin, inda ya ce jami’an NCoS uku sun samu munanan raunuka.

“Jimillar fursunoni 879 ne suka tsere daga wurin a lokacin da aka kai harin. Ya zuwa wannan rahoto, an sake kama mutane 443, fursunoni 551 a halin yanzu suna tsare, fursunoni 443 na hannunsu.

“ Fursunoni hudu sun mutu sannan 16 sun samu raunuka daban-daban kuma ana kula da su a halin yanzu. Sai dai ana ci gaba da kokarin kamo dukkan fursunonin da suka gudu,” inji shi.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy