Babu Dalibar Data Jikkata Ko Rasa Rai Sakamakon Gobarar GGC – Lauratu Diso

0

Babu Dalibar Data Jikkata Ko Rasa Rai Sakamakon Gobarar GGC – Lauratu Diso - Dimokuradiyya

Babbar sakatariyar a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Hajiya Lauratu Ado Diso ta yabawa jami’an hukumar kashe gobara ta Kano da tarayya, bisa daukin gaggawa da suka kai makarantar yan mata ta GGC Kano.

Lauratu ta gode musu ne sakamakon hanzarta kashe wutar da ta tashi a daya daga cikin dakunan kwanan daliban, wadda ta kama a farkon Makon nan.

Ta bayyana hakan yayin da take ziyarar duba wajen ginin da gobarar ta tashi, a juya Talata, inda ta bayyana godiya ga Allah sakamakon yadda gobarar ta takaita.

Daga nan sai ta bayar da umarnin sauyawa daliban da suke Matsugunin da ya kama da wuta zuwa wani Dakin kwanan na daban.

Ta kara da cewa gwamnati na ci gaba da kokarin ganin an dauki duk bayanan da suka kamata domin sanin abun yi, biyo bayan asarar kayayya masu yawa da daliban suka yi.

Ta ce har yanzu dalilin rashin gobarar ba a kai ga gano shi ba, amma kuma sanadiyyar gobarar babu dalibar da ta jikkata, kuma ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin nata.

Daga nan sai ta bukaci iyaye da su kwantar da hankali tare da watsi da duk wata jita jita da za a ci gaba da yaɗawa kan gobarar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy