Video:-/Bayahude Ya Musulunta Bayan Yaga Annabi A Mafarki, Allahu-akbar

0


Labarin Yau Daga Majiyar Mu Presshausa Dailyupdate.

A kwanakin baya, Sanford Pass, wanda yake Bayahude ne ya karbi addinin Musulunci, sannan ya wallafa labarin yadda aka yi ya karbi addinin Musuluncin a shafukan sadarwa.

Sanford ya bayyana yadda ya Musulunta a wata hirar da aka yi da shi ta bidiyo mai suna ‘TheDeenShow’.

A kasa dai an yi hira da shine a wata tashar YouTube mai suna Digital Mimbar, domin a san abubuwan da ya karu da su bayan ya Musulunta.

Da aka tambayi Sanford abinda ya jawo hankalin shi ya Musulunta, ya ce shi ba shi da wani ilimi akan addinin Musulunci. Bai taba haduwa da wani Musulmi bama a rayuwar shi. Sai dai watarana da daddare yayi mafarki da yake da dangantaka da Musulunci, wanda tun daga lokacin rayuwar shi ta canja baki daya.

Related Post:-

Sanford ya ce yaga wani mutumi, amma bai ga ainahin fuskar shi ba. Amma dai ya ce ya tabbata mutumin yana kallon shi ne kuma yana murmushi.

Tun daga wannan rana, sai ya sanar da wani Limamin Masallaci game da mafarkin shi. Limamin ya fahimci mafarkin na shi, inda ya sanar da shi cewa Annabi Muhammad (SAW) ne ya kai masa ziyara.

Sanford wanda yake da shekaru 71 a duniya, ya ce yaga mutumin sanye da rawani na zinare, sannan kuma sauran kayan jikinshi kuma fari ne tas.

Kusa dashi haske ne sosai, hakan ya sanya na kasa ganin fuskarshi. Ya kara da cewa a lokacin sai yaji ya samu nutsuwa a ran shi. Sanford ya ce bayan wannan mafarki na shi yana jin dadi sosai a ranshi.

Ya kuma bayyana cewa ya kasa yiwa mutane bayani dangane da mafarkin nashi. Saboda a duk lokacin da suka saurare shi, sai suce yaje ya gana da Allah ne.

Duk da dai bai cigaba da bayani ba, ya ce yana da tabbacin abinda ya gani gaskiya ne.

Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Sharing is Awesome, Do It!

Share this post with your friends
close-link