Bayan Gaza Zama Dan takarar shugaban kasa a PDP, Bala Muhammad Ya Sami Tikitin Gwamna

0

Bayan Gaza Zama Dan takarar shugaban kasa a PDP, Bala Muhammad Ya Sami Tikitin Gwamna - Dimokuradiyya

An ayyana gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.

A yau ne aka sake zaben fidda gwani a otal din Zaranda da ke Bauchi.

Kuma Shugaban kwamitin zaben Murtala Damagum a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben ya bayyana cewa akwai wakilai 656 a jihar.

Ya bayyana cewa 20 daga cikin wakilan akwai wakilai na kasa daga kowace karamar hukuma 20 na jihar.


Download Mp3

Damagum ya kara da cewa sauran wakilai 636 da suka rage a gundumomin zabe 323 na jihar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Damagum, ya ce wakilai 10 ba su halarta ba, 650 kuma suka samu amincewa yayin da wakilai 646 suka kada kuri’a.

A cewarsa, gwamna Mohammed ya samu kuri’u 646 da aka kada.

A jawabinsa na godiya, Mohammed ya bayyana godiyarsa ga sakataren gwamnatin jihar, wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na farko da aka gudanar a makon da ya gabata, amma ya sauka domin kauran Bauchin ya hau.

Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa an ayyana Ibrahim Kassim a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na farko da aka gudanar a makon jiya amma ya sauka domin share fagen zaben ga gwamna Mohammed.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy