- Advertisement -

Bayan Korar Malamai Sama Da 2,000, Zan Dauki Wasu 10,000—– El-Rufa’i

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana kudurinta na sake daukan malaman makarantar firamare dubu goma 10,000 da za su maye gurbin wadanda aka sallama don ganin an cike gibin malaman da aka kora da kuma karatun yaran.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr. Hadiza Balarabe ce ta bayyana hakan a jiya laraba a garin Kaduna, yayin kaddamar da kayayakin aiki ga daliban makarantun firamare na gwamnati dubu hudu da dari biyu da sittin da Kuma wuraren koyarwa dari takwas da talatin da takwas.

- Advertisement -

Ta Kuma Kara da cewa idan har aka baiwa ‘ya’yan talakawa litattafan karatu to tabbas za su mai da hankali ga karatu sosai, yayin da kuma ta cigaba da nuna cewa muddin za a baiwa yaran littattafan karatu za su fi mai da hankali wajan samun ilmi mai inganci.

Korar malaman da gwamnatin jihar ta yi ta kira shi korar “marasa kwarewa” na shekara-shekara a jihar Kaduna a yunkurinta na tsaftace fannin ilimi.

Idan ba’a manta ba, A ranar 19 ga watan Yuni ne gwamnatin jihar ta sanar da korar malaman makarantun firamare dubu biyu da dari uku da hamsin da bakwai (2,357) saboda abun da takira, rashin cin jarabawar da gwamnati ta yi musu.

- Advertisement -

Sai dai ko a shekarar 2018, gwamnatin jihar ta kori wadansu malamai kimanin dubu ashirin da daya da dari bakwai da tamanin (21,780), saboda faduwa jarrabawa makamanciya hakan, yayin da aka sake korar wasu dari biyu da talatin da uku (233) a watan Disambar shekarar 2021, bisa zargin gabatar da shaidar karatu wato satifiket na bogi.

Kazalika da take jawabi a wajen kaddamar da taron rabon kayayyakin karatu ga dalibai a makarantun firamare na gwamnati dubu hudu da dari biyu da sittin (4,260) da kuma cibiyoyin koyo dari takwas da talatin da takwas ,(838) a kaduna, mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe, ta ce gwamnati za ta ci gaba da sallamar malaman da ba su cancanta ba a makarantun gwamnati ba tare da wani adadi ba. Ko wani abu da zai dakatar da ita ba.

Har wa yau Dakta Hadiza ta ce, ingantacciyar koyarwa na da matukar muhimmanci wajen tantance sakamakon karatun yara, tana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta kyale ‘ya’yan wasu ’yan kalilan kawai su kwashe ribar da ilimi ke samarwa ba.

- Advertisement -

Ta kuma kara da cewa, ‘ya’yan talakawa suma sun cancanci ƙwararrun malamai, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace gwamnati ta tabbatar sun samu.

A cewar ta Dr. Hadiza Balarabe ta ce gwamnatin jihar ta gyara makarantun firamare da sakandare na gwamnati sama da dari biyar 500 tare da samar da shinge a makarantu da dama kamar yadda hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka bukata domin kulawa da ilimin yaran.

karshe ta bayyana cewa za a raba kayayakin aikin ne karkashin Shirin BESDA da gwamnatin jihar ta samar.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy