Bincike: Sunayen da ake yaɗawa na Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa na APC da aka soke, na ƙarya ne

0

Bincike: Sunayen da ake yaɗawa na Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa na APC da aka soke, na ƙarya ne - Dimokuradiyya

Jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC wadanda aka kora sakamakon gaza cancantar su na yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani duk kuwa da cewa sunayen na Bogi ne.

Jerin sunayen mutum 23 ya nuna cewa ’yan takara 10 da suka hada da Robert A. Boroffice da Uju Ken-Ohanenye da Tunde Bakare da Bola Tinubu da Ahmed Rufai Sani da Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio da Rochas Okorocha da Tein Jack-Rich da kuma Ikeobasi Mokelu ne kwamitin tantance yan takarar ya kora.

Kwamitin tantance yan rakarar shugaban kasa bisa jagorancin Chief John Odigie Oyegun gabanin babban taron jam’iyyar da za a yi a ranar 6-8 ga watan Yuni, 2022 ne ya tabbatar da rashin cancantar su.

Tabbatarwar da Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa gaskiya kwamitin tantance masu neman takara bai ambaci sunayen wadanda ake yaɗawa su 10 ba, cewa ya soke cancantar su.


Download Mp3

Sai dai shugaban kwamitin, Cif Odigie Oyegun, bai bayyana sunayensu ba a lokacin da yake gabatar da rahoton ga kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Juma’a.

Jerin Sunayen Yan Takarar Shugaban kasa da aka Kora na Bogi

A yayin gabatar da rahoton, Oyegun ya lura cewa 13 ne kawai daga cikin 23 da kwamitin ya tantance suka cancanta tsayawa domin tsayawa takarar fidda gwanin a cikinsu.

Yanzu dai gaskiya ta bayyana cewa ba a tantance mutane 10 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ba, amma ba a bayyana sunayen wadanda abin ya shafa ba.

Don haka, labarin dake zagaye a intanet na karya ne, ba na hukuma ba kuma yakamata a yi watsi da shi.

An yi wannan binciken gaskiyar tare da haɗin gwiwar Cibiyar Dimokuradiyya da Ci gaban Al’umma (CDD).

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy