Buhari baya da ra’ayin kawo ƙarshen Ƴan Ta’adda a Najeriya — Inji Ortom
Gwamnatin Tarayya bata da ra’ayin kawo ƙarshen Ƴan Ta’adda — Inji Ortom
Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom ya shaidawa Ƙasashen Waje cewa Gwamnatin Tarayya bata da ra’ayin ɗaukar mummunan mataki akan Ƙungiyoyin Ƴan ta,adda.
Yayi kira ga Kasashen Duniya dasu matsawa Gwamnatin Tarayya domin ganin ta magance ta’addancin makiyaya a ƙasar ba tare Addini ko ɓangaranci.
A cewar Sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labarun sa ya fitar Nathaniel Ikyur, Ortom Yayi wannan kiran ne a lokacin da ya karɓi tawaga daga Majalisar Burtaniya akan bada dama ta fuskar sha’anin Addini a gidan Gwamnan Benue dake Asokoro, Abuja.
Sanarwar tace “Gwamnan yace kasancewar ƙasa mai addinai da Al,adu kala-kala, Gwamnatin Tarayya dake da alhakin an kiyaye su, ya kamata ta ɗauki abun dagaske ba kamar yadda take yi ba.
“A cewar Gwamna Ortom, kasawar Gwamnatin Tarayya na ɗauki mummunan matakin gaggawa kan ƴan ta’adda a Ƙasar na tsawon Shekaru, yanzu wasu ƙungiyoyin musulunci na son kawo karɓe iko da Ƙasar, wanda dole a kawo ƙarshen haka.
