Buhari Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Sarki Mafi Dadewa A Karagar Mulki A Jihar Zamfara

0

Buhari Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Sarki Mafi Dadewa A Karagar Mulki A Jihar Zamfara - Dimokuradiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin rasuwar sarkin Zamfara wanda ya fi dadewa akan karagar mulki, Sarkin Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu, Alh. Ahmad Umar.

Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana rasuwar a matsayin “gibin da ba za a iya cikewa ba.”

Shugaba Buhari, wanda ya ce “Shugaba mai kirki da kulawa ya bar mu,” ya kara da cewa shekaru 61 da marigayin ya yi a kan karagar mulki ya shaida ci gaban al’ummarsa, wanda a saboda haka za su ci gaba da yaba masa.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma bukaci al’ummar masarautar Kwatarkwashi da jihar Zamfara baki daya da su jure hakurin wannan rashi da jajircewa.


Download Mp3

A WANI LABARIN KUMA, Hukumar hana fasa qwauri ta kasa reshen Kano da Jigawa ta bayyana shiryawar ta domin aiki da kungiyar yan jaridu ta Jihar Kano, don tafiya tare a ayyukan da take.

Kwanturolan Hukumar Muhammad Umar ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi Bakuncin shugabanninnm kungiyar a ofis dinsa.

Muhammad Umar ya bayyana yan jarida a matsayin wani kashin baya wajen samar da ci gaban al’umma, wanda kuma suke da tasiri wajen sanar da mutane abun da ke faruwa, kuma hadakar domin tafiya tare zata taimakawa hukumar Kwastom din kan irin aikace aikacen da take yi.

Anasa jawabi mataimakin Kwanturolan Hukumar M.A Hassan ya ce hukumar a koda yaushe na tabbatar da cewa jami’an ta maza da mata na aiki yadda doka ta tanadar musu.

Baya ga haka, ya bayar da tabbacin cewa duk wanda aka samu cikin jami’an su da laifin taka doka, to kuwa Doka shima zata taka shi daidai yadda ya debo.

Da yake jawabi tunda fari, sakataren kungiyar ta Chapel Comrade Musbahu Aminu Yakasai, yace sun je hukumar ne domin jaddada alakar aiki a tsakanin su da hukumar.

Ya kuma kara da cewa a shirye suke domin ci gaba da sanar da al’umma irin aikace aikacen hukumar, da nufin al’umma su ci gaba da basu hadin kai.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy