Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Wasu Yarjejeniyoyi 9,MoU Da Kasar Sipaniya

0

Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Wasu Yarjejeniyoyi 9,MoU Da Kasar Sipaniya - Dimokuradiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai bukatar shugabannin kasashen duniya su hada kai tare da tsara hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da ke kunno kai a fadin duniya.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a birnin Madrid na kasar Spain, a fadar sarauta a lokacin da yake ganawa da mai martaba Sarki Felipe VI.

Sarkin ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai muhimmanci tare da bayyana cewa yana fatan samun damar ziyarta.

Shugaban ya mika godiyarsa ga mai masaukin baki bisa gayyatar da aka yi masa tare da sanar da shi abubuwan da ke faruwa a gida, ciki har da shirye-shiryen tunkarar babban zabe na 2023.

A wani taron da ya yi da shugaba Pedro Sanchez, Buhari ya ce Najeriya na fatan kara huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Najeriya ya yabawa takwaransa na kasar Spain bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci a yankin kudu da hamadar Sahara musamman a kasar Mali.

A cikin jawabinsa, Sanchez ya shaidawa Buhari cewa Najeriya ta kasance babbar abokiyar huldar kasashen Turai tare da bayyana shirin kara dankon zumunci.

Shugabannin gwamnati da ministocinsu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin guda tara da yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).

Sun hada da Yarjejeniyar Taimakon Shari’a a kan Al’amuran da suka shafi Laifuka, Canja Mutane Hukunci, Fitar Dasu; Hadin gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci.

Sauran sun haɗa da Yawon shakatawa, Wasanni, Lafiya, Yaƙi da COVID-19, Kimiyya da Ƙirƙiri.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy