Browsing Category

Kannywood

Kannywood Entertainments News Updates For Breaking News.

- Advertisement -

Masha Allahu:; Shugaban Tace Fina-finai Afakallahu Zai Angwance da Jaruma Rukayya Dawayya

Kamar dai yadda kuka sani jaruman massage Kannywood suna auran abokan aikin nasu tun daga shekarun baya da suka wuce yanzu ma ana sa ran shugaban hukumar tace fina-finai na Jihar Kano Isma’il Na’Abba Afakallahu Zai Angwance da Jaruma a Masana’antar Shirya Fina finai Hausa Rukayya Dawayya. Ga bidiyon nan ku kalla dan jin cikekken labarin game da batun auren nasu. https://www.youtube.com/watch?v=2FP06Q6DXhQ  

Bidiyon:; Barka da Sallah daga jaruman kannywood da Iyalan su

Hotuna da bidiyoyin barka da sallah daga jaruman masana’antar Kannywood tare da iyalen su, cikin su akwai mawaki rarara,  da jarumi lawan Ahmad, sai jarumi ramadan booth, sai sadik sani sadik, malam Ibrahim sharukan, su halima atete، da aisha humaira dadai sauran su muna addu ar Allah amshi ibadun mu baki daya ameen Ga bidiyon nan ku kallah:; https://www.youtube.com/watch?v=Uk4qIt5cy8Q  
- Advertisement -

Yadda Starlinks za su amfani Kannywood – Abdulkareem Muhammad

Alhaji Abdulkareem Muhammad BABBAN furodusa a Kannywood kuma shugaban kamfanin shirya finafinai na ‘Moving Image’ da ke Kano, Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa majalisar shirya finafinai cikin harsunan gado da ke Inugu mai suna ‘Starlinks Movie Africa’ za ta iya amfanar masana’antar Kannywood ta hanyoyi da dama. Alhaji Abdulkareem, wanda kuma shi ne shugaban masu shirya biki da kasuwar baje-kolin finafinan da ake shiryawa cikin harsunan gado na Afrika a Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film…

Abubuwa 3 Da Za A Rika Tunawa Da Daraktan ‘Izzar So’ Nura Mustapha Waye

A karshen makon da ya gabata ne Allah ya yi wa Daraktan fim mai dogon zango na “Izzar So” Nura Mustapha Waye rasuwa. Jarumin fim din na “Izzar So” Lawan Ahmad ne ya bayyana rasuwar Nura a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi Aminiya ta rawaito. Nura Mustapha, darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana’antar ta Kannywood. Fim din na Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya. Kiyasi da aka yi a baya-bayan…

Hira da Yan’uwan Nura Mustapha Waye Sun Fadi Yadda Nura ya rasu

Hira da yan uwana marigayi Nura Mustapha Waye yan uwana nasa sun bada labarin yadda marigayi Ya rasu daya daga cikin yar uwar sa tace nura ya shigo gida ya samu mahaifiyarsa ya tashe ta yace ga nama na sayo miki umma tashi kici haka ta tasshi taci sai yace umma me kike so bayan wannan tace ba komai saiya dauko dubu biyar ya bata yaci ta daina fita. Daga nan nura ya tashi ya shiga daki ya kwanta daga nan matar sa tazo tashin sa sai ta mai magama taga yaki amsawa sai tayi yunkurin tashin sa sai gashi taga alamaun ba…
- Advertisement -

Hira Da Mahaifiyar Nura Mustapha Kan Rasuwarsa

Abin Tausayi! Mahaifiyar Marigayi Nura Mustapha Ta Bayyana Sanadiyyar Rasuwar Yaron Nata Da Irin Babban Rashin Da Tayi, Masana’antar KannyWood Ta Girgiza Sosai Da Rasuwar Daraktan Shirin IZZAR SO, Nura Mustapha Waye, Inda Mutuwar Tashi Ba Iya Iyalansa Da Yan Uwansa Akayi Ba. Har Masana’antar KannyWood Suma Wannan Rashin Ya Jijjigasu. Nura Mustapha Ya Rasu Ne Ranar Lahadi Uku Ga Watan Bakwai Na Shekarar Dubu Biyu Da Ashirin Da Biyu. Inda Ya Rasu Da Misalin Karfe Goma Sha Daya. Mahaifiyarsa Da Wasu Jaruman Masana’antar…

Babu abinda ya fi min dadi idan na tuna idan na mutu zan hadu da ANNABI SAW Kalaman Nura Na Karshe

Nura Mustapha Waye Darakta ne a masana’antar Kannywood ya rasu a safiyar yau na lahadi Mustapha Waye ya kasance wanda yake wakiltar shirin Izzar kuma duk wanda yake kallon wannan shirin yasan nura Mustapha Waye cikekken masoyin manzon Allah S. A. W ne. Kafin rasuwar daraktan abubuwa da dama sun faru na abin alja bi na magana dayayi me ratsa zuciya Mustapha akwai lokacinda ya wallafa wani rubu a shafin sada zumunta na Facebook inda yake cewa. Babu abinda ya fi min dadi idan na tuna idan na mutu zan hadu da ANNABI SAW…
- Advertisement -

Innalillahi wa’innah Ilaihir Raj’un Yanzun Nan Allah Yayiwa Mustapha Waye Rasuwa Daraktan Izzar so

Yanzu muke samun labarin rasuwar daraktan shirya fim ɗin Izzar so wato Mustapha Waye rasuwa, kamar yadda producer ɗin fim Lawan Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook. Allah ya karbi rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO, za ayi jana’izarshi ƙarfe 11 na safe Insha Allah, Allah Ya yafe masa kurakuransa Amin, Allah yasa idan tamu tazo mu cika da imani Amin”, Inji shi. Please Muna Neman Addu'ar Ku Da Dukkan 'Yan Uwa Musulmai Baki Daya. Allah Ya Jikanshi Da rhm.

An sake cire Ummi Alaqa daga shirin dadinkowa

Habiba aliyu dai wacce kuka sani da ummi alaqa watannin baya aka samun labarin an cire ta daga cikin shirin alaqa wanda hakan ya tada cece-kuce a shafukan sada zumun ta. Yanzu kuman kamar yadda aka dawo haska shirin dadin kowa a jiya asabar sai aka samu labarin an sake cire ta a cikin shirin dadin kowa kuma, a cikin shirin dadin kowa habiba ta kasance yar alkali dikko kuma budurwar badaru. Yanxu ga bidiyon nan ku kalla danjin muhimiyar abunda yasa aka cire ta daga cikin shirin dadin kowa.…

Furodusa Isma’il FKD ya zama angon A’isha Umar

Ango Isma'il FKD a tsakiyar wasu daga cikin abokan sana'ar sa A YAU Juma’a, 24 ga Yuni, 2022 aka ɗaura auren matashin furodusa Isma’il Usman, wanda aka fi sani da suna Isma’il FKD, da sahibar sa A’isha Umar. An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:25 na rana, bayan idar da sallar Juma’a a masallacin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da ke Tudun Wada, Kaduna, a kan sadaki N100,000. ‘Yan fim da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Ibrahim Al-Imash, Sabi’u M. Gidaje, Abdullahi Abu Uku, Yusuf Waza-Waza, Haruna M. Gidaje, Aminu Haske,…
- Advertisement -

Mawaƙi Sufin Zamani ya ba ‘yan fim haƙuri, ya wanke su da baiti biyu

Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) a cikin bidiyon ban-haƙuri da ya saki a yau MAWAƘIN nan wanda ya ɓata mata ‘yan fim a wata waƙa, Malam Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani), ya bayyana nadamar abin da ya yi tare da ba su haƙuri, kwana ɗaya bayan ya samu beli daga Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS). Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda hukumar ta tsare shi daga shekaranjiya zuwa jiya sakamakon ƙarar sa da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta kai mata. A daren yau Sufin Zamani ya saki…

Tarihin Rayuwar Hamisu Breaker Dorayi, (“Biography Networth Of Hamisu Breaker”)

Barkan Ku Da Zuwa Wannan Shafi Many Na Pressloadedng.com Shafin Dake Kawo Maku Labarai Cikin Harshen Turanci Da Kuma Hausa, Ayau Munleka A Masana'antar Kannywood Inda Muka Zanata Da Fitacen Mawaki Wato (" Hamisu Breaker Dorayi ") Ga Rahoton Da Abba Muhammad Kaduna Ya Ruwaito Mana A Yayin Zantawar sa Da Mawakin Hamisu Breaker. WANENE HAMISU BREAKERHamisu yakasance Mawakin hausa kuma jarumi Wanda yayi fice a fadin Nigeria musamman arewa dama nahiyar Africa gaba daya. cikakken sunansa Hamisu Sa’id yusuf Amma

Malam Zaidu Gidan Badamasi, Ya Magantu Akan Yin Kuskure

Fitaccen jarumi kuma furodusa na masana’antar Kannywood, Aminu Shehu Usman, wanda aka fi sani da Aminu Mirror ya bukaci mutane su dinga yi musu gyara idan sun ga sun yi kura-kurai, Daily Trust ta ruwaito. A wata tattaunawa da Daily Trust tayi da shi, Aminu, wanda yanz aka fi sani da Malam Zaidu daga fim din da yayi na Gidan Badamasi, ya ce ya samu nasarori masu tarin yawa daga shigarsa masana’antar zuwa yanzu. Ya fara gabatar da kansa inda yace an fi saninsa da Aminu Mirror a shekarar 1999 zuwa 2000 da doriya, amma abin…
- Advertisement -

Abin da ya sa za a naɗa ni Kogunan Ɗanja ranar Asabar mai zuwa – Ashiru Bazanga

Katin gayyatar zuwa naɗin Ashiru Sani Bazanga FITACCEN jarumi kuma furodusa, Malam Ashiru Sani Bazanga (Sawun Keke), ya bayyana farin ciki kan bikin naɗa shi sarautar Kogunan Ɗanja da za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 18 ga Yuni, 2022, a fadar Sarkin Kudun Katsina da ke garin Ɗanja a Jihar Katsina. Sarkin Kudun Katsina, Hakimin Ɗanja da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja, Alhaji M.T. Bature, shi ne zai naɗa shi tare da wasu manyan mutane da misalin ƙarfe 10:00 na safe.A hirar sa da mujallar Fim, Bazanga ya ce tarayyar sa da Sarkin…

Zaɓen 2023: Rarara ya waƙe Tinubu, ya saka gasar bidiyon waƙar inda zai raba motoci

Daga hagu: Rarara, Tinubu, Baban Chinedu da El-Mu'az Birniwa FITACCEN mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya taya ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe zaɓen fidda-gwani da ya yi a ranar Asabar ta makon jiya. Haka kuma ya rera masa waƙa tare da bayyana gasar bidiyo inda zai ba gwaraza kyautar motoci da manyan wayoyi samfurin Iphone-13. Rarara, wanda shi ne shugaban mawaƙan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na Arewa, ya miƙa saƙon taya murnar…

Rayya Kwana Casa’in Itama Ta fara wakan Hip pop Tabi Sahun Safara’u

Jaruma surayya aminu wacce kuka fi sani da suna rayya na cikin kwana casa’in itama tazo da wani sabon salo na wakar zamani wato hausa hiphop. Idan baku manta ba kwanakin baya haka safara’u itama ta rero wassu wakokin ta wanda hakan ya janyo cece kuce a shafukan sada zumunta na zamani kuma ita safara’un daga cikin fim din casa’in ta fara fim. To yanzu ma rayya nan ta fito da nata wakar fatan dai nata bazata ayi abunda zai janyo cece-kuce ba a gari. Ga bidiyon wakar nata ku kalla:;…
- Advertisement -

Hukumar DSS ta tsare mawaƙi Sufin Zamani kan cin zarafin matan Kannywood

HUKUMAR Tsaron Ƙasa (Directorate of State Security, DSS) shekaranjiya ta tsare wani mawaƙi mai suna Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) na tsawo kwana ɗaya sakamakon ƙarar sa da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta kai mata kan cin mutuncin da ya yi wa matan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood a wata waƙa Fim magazine ta rawaito. MOPPAN, a cikin wata takardar sanarwa da kakakin ta, Malam Al-Amin Ciroma, ya fitar a yau, wadda aka miƙa wa mujallar Fim, ta ce kai ƙarar ya biyo bayan ƙorafin…

El-Mu’az Yayi Kyautar Zungureriyar Mota Ga Mawaƙi Baban Kausar

A sama: Sagir Baban Kausar (a hagu) tare da El-Mu'az Muhammad Birniwa. A ƙasa kuma motar da aka yi kyautar da ita ce SANANNEN mawaƙin nan da ke Kaduna, Sagir Ɗanyaro (Baban Kausar), ya bayyana fitaccen mawaƙin siyasa El-Mu’az Muhammad Birniwa da cewa shi mutum ne da ya ke iya yi wa mutane hidima da duk abin da ya ke da shi ba tare da ya damu ba, kuma “mai irin wannan hali duk abin da ya yi ba zai zama abin mamaki ba.” Baban Kausar ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim sakamakon kyautar dalleliyar mota ƙirar…

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy