Chelsea ta amince Lukaku ya bar Stamford Bridge

0

Romelu Lukaku zai kammala komawarsa Inter Milan a wannan makon, yayin da Chelsea ke gab da cimma matsaya kan kudin cinikin dan wasan.

Kulob din na Seria A ya kara yawan tayin sa na farko na fam miliyan 6 zuwa fam miliyan 8.5 tare da kari.

A cewar jaridar Daily Mail, an shirya sake wata ganawa tsakannin kungiyoyin biyu ta hanyar kiran waye na bidiyo a ranar Litinin.

Chelsea ta tattauna yiwuwar rangwame ga ‘yan wasan Inter a wani bangare na tattaunawa da Milan wanda Skriniar da Denzil Dumfries na cikin wadanda ake tunanin za’a iya sanyasu a cinikin

Duk da haka, ana tsammanin zai zama yarjejeniyar lamuni madaidaiciya kamar yadda akafa tsara cinikin tun farko.

A wani labarin kuma na daban.

Da-Dumi-Dumi: Gwamnatin Kaduna ta kori shugaban NUT da wasu malamai 2,356


Download Mp3

Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna ta ce ta kori malamai 2,357 da suka fadi jarabawar cancanta da aka gudanar kwanan nan.

Mai magana da yawun hukumar, Hauwa Mohammed, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Kaduna, ta ce hukumar ta gudanar da gwajin cancanta ga malamai sama da 30,000 a watan Disamba 2021.

Ta ce malaman makarantun firamare 2,192 da suka hada da shugaban kungiyar malamai ta Najeriya Mista Audu Amba, an kori su ne saboda kin zana jarabawar cancantar.

Mohammed ya kuma bayyana cewa an kori malamai 165 daga cikin 27,662 da suka zana jarabawar cancantar aikin saboda rashin nuna kwazo.

A cewarta, za a saka ƙwararrun malamai a cikin shirye-shiryen haɓaka ƙwararrun malamai don haɓaka ƙarfinsu don isar da ingantaccen koyarwa ga ɗalibai.

Mohammed ya ce malaman da suka samu maki tsakanin kashi 40 zuwa 74 cikin 100 ba su cika samun mafi karancin maki ba, inda ya ce za a sake ba su dama ta biyu don inganta kwarewarsu.

A shekarar 2018 ne gwamnatin Kaduna ta kori malamai 21,780 da suka fadi jarabawar cancanta, sannan ta maye gurbinsu da wasu 25,000 da aka dauka ta hanyar kwazo.

A watan Disambar 2021, Hukumar ta kuma kori malamai 233 bisa zargin mallakar takardun bogi.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy