Da Ɗuminsa: Bayan Janye wa Tinubu, Akpabio ya samu Tikitin Takarar Sanata a APC
Da Ɗuminsa: Bayan Janye wa Tinubu, Akpabio ya samu Tikitin Takarar Sanata a APC.
Tsohon Ministan Niger Delta Godswill Akpabio ya samu Tikitin Tsayawa Takarar Kujerar Sanata mai Wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a Jam’iyyar APC.
Akpabio Wanda ya janye wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a lokacin Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar, ya samu nasara da ƙuri’u 478.
Daga cikin Deliget 540, an tantance 512 inda Sir Akpan keda ƙuri’a 1, DIG Ekpo Udom Wanda ke yaci Zaɓe na Fidda Gwani nada ƙuri’u 3, a yayinda kuri’u 11 suka lalace.
Da yake jawabi a daren ranar Alhamis a cibiyar Tallafawa ta Godswill Akpabio a Ƙaramar Hukumar Ikot Ekpene, inda aka gudanar da Zaɓe, Akpabio ya godema Al’umma da suka zaɓe.
A nashi jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC Mr Stephen Ntukekpo yace Uwar Jam’iyyar ta Ƙasa ta bashi umarni ya gudanar da zaɓen, yana mai bayyana wasu dalilai marasa dalili.
