- Advertisement -

Da Ɗuminsa: Najeriya ta sanya ranar fara Jigilar Maido da Alhazan ta

0

Da Ɗuminsa: Najeriya ta sanya ranar fara Jigilar Maido da Alhazan ta - Dimokuradiyya

Da Ɗuminsa: Najeriya ta sanya ranar fara Jigilar Maido da Alhazan ta

- Advertisement -

Kwaso Alhazan Nijeriya daga Kasar Mai Tsarki, Saudiyya zai fara daga ranar Juma’a 15 ga watan Juli na Shekarar 2022.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Aikin Hajji na Najeriya Zikirullah Kunle Hassan ya bayyana haka a ranar Talata a lokacin taron kammala aikin Arfa daya ke wakana a Makkah, Ƙasar Saudi Arabia.

“Biyo amince da Hukumar GACA, za’a fara Jigilar maido da Alhazan Nijeriya a ranar Juma’a 15 ga watan Juli”, Inji Shugaban Hukumar

- Advertisement -

Gidauniya ta bata taɓa Tilasta Kiristoci su karɓi Musulunci Ba — Martanin Ganduje Ga Babachir

Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya Musanta kalaman tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal cewa Gidauniyar Ganduje ana amfani da’ita domin tilasta Kiristoci shiga Musulunci.

A lokacin da yake nuna ƙin amincewar sa ga Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Bola Tinubu Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Lawal ya ƙalubalanci Ganduje na yunƙurin musuluntar da Najeriya.

- Advertisement -

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar yace Gidauniyar an kirkire ta da manufar Tilasta Kiristoci karɓar Musulunci.

Amma a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaru Malam Muhammad Garba ya fitar a madadin Ganduje, yace wannan Kalamai ƙarya ce tsantsagwaron ta.

Yace Musulunci yana ba kowa dama ya zaɓi Addinin da yake so, ya na baiwa Waɗanda ba musulmai ba dama ta bangaren tattalin arziki, Al’ada da Shuwagabanci.

- Advertisement -

Yace ba’a taɓa samun wani Kirista an tilasta shi karɓar Musulunci ba, domin tana akan koyarwar musulunci.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy