DA DUMI-DUMI: An Garkame Majalisar Dokoki Ta Kasa Yayin Da Kungiyar PASAN Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

0

DA DUMI-DUMI: An Garkame Majalisar Dokoki Ta Kasa Yayin Da Kungiyar PASAN Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani - Dimokuradiyya

Kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin tarayyar Najeriya (PASAN) ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, inda ta bukaci da a yi musu kwaskwarima kan yanayin aikinsu.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a watan Mayun shekarar 2020 PASAN ta rubutawa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai wasika, Femi Gbajabiamila, suna roƙonsu da su shiga cikin rikicin da ya biyo bayan wani shiri da ake zargin an yi na dakatar da aiwatar da dokar yanayin hidima ga membobin.

Sai dai wani mamba a kungiyar ta PASAN EXCO da ya zanta da Jaridar DAILY POST bisa sharadin sakaya sunansa, ya ce har yanzu ‘yan majalisar ba su aiwatar da sharuddan hidimar ba.

Ya ce mambobin kungiyar sun yanke shawarar rufe ayyukan Majalisar har sai an biya musu bukatunsu.


Download Mp3

Ya ce, “Bangarori biyu, na Majalisar Dokoki ta Kasa da na Majalisar Tarayya, sun amince gaba daya cewa za mu shiga yajin aikin da ba a taba gani ba, saboda muna da yarjejeniyar fahimtar juna, MoU da aka rattaba hannu, amma hukumar ta ki aiwatar da yarjejeniyar.

“An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2020, amma har ya zuwa yau, ba a aiwatar da komai ba.

An yi wani mataki na daidaita ma’aikata kan mafi karancin albashi, Gwamnatin Tarayya ta fitar da asusun hakan amma har zuwa yau, Majalisar Dokoki ta kasa na bin bashin mafi karancin albashin”.

A lokacin da Jaridar DAILY POST ta ziyarci ofishin Majalisar Dokoki ta kasa da ke Utako,taga ginin yana kulle yayin da aka ga jami’ai na yawo a yankin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy