Da dumi-dumi: Atiku ya karbi takardar shaidar taka takara a jam’iyar PDP

0

Da dumi-dumi: Atiku ya karbi takardar shaidar taka takara a jam’iyar PDP - Dimokuradiyya

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sen. Iyorchia Ayu (L), yayin da yake mika takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar (R) a Abuja ranar Laraba (1/6/22). Tare da su akwai Sakataren Yada Labarai na PDP na Kasa, Sen. Sam Anyawu.

Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar PDP ya gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.


Download Mp3

Mista Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ne a yayin babban taron jam’iyar kasa na musamman da aka gudanar a Abuja a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun 2022 bayan ya samu kuri’u 371 inda ya doke wasu ‘yan takara 11 a suka fafata a zaben.

Gwamnoni, ’yan takarar gwamna, ’yan takarar shugaban kasa, mambobin kwamitin amintattu na BoT, ‘yan majalisar wakilai ta kasa, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar da duk masu ruwa da tsaki ne suka halarci bikin na musamman.

An gudanar da taron ne a ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy