Da Dumi-dumi: Gwamnan Jigawa Badaru Ya Janye Daga Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC

0

Da Dumi-dumi: Gwamnan Jigawa Badaru Ya Janye Daga Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC - Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya janye daga tsaywa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Badaru ya fice daga zaben fidda gwanin da aka shirya yi ranar litinin bayan gwamnonin APC 10 sun goyi bayan sauya shekar takarar zuwa yankin Kudu a 2023.

A yanzu haka dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana ganawa da ‘yan takarar jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.


Download Mp3

Buhari, wanda ya dawo daga taron ECOWAS na musamman da aka yi sa’o’i da suka wuce, zai gana da akalla mutane 23 da aka amince da su a matsayin wadanda suke neman tsayawa takarar shugabancin kasa.

Masu fatan tsayawa takarar shugabancin kasar dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Gwamna Yahaya Bello (Kogi), Dave Umahi (Ebonyi), Kayode Fayemi (Ekiti), tsohon ministan harkokin Neja Delta, Goodwill Akpabio, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da dai sauransu.

Yayin da ya rage sa’o’i 48 a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, taron zai ta’allaka ne kan zaben dan takarar bisa tsarin yarjejeniya.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa shugaban kwamitin tantancewar, Dr John Oyegun, a ranar Juma’a ya shaidawa manema labarai cewa kashi 99 cikin 100 na masu son tsayawa takara suna goyon bayan yarjejeniya.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy