Da-Dumi-Dumi: Gwamnatin Edo ta dakatar da ASUU, ta ba da umarnin a cigaba da karatu

0

Da-Dumi-Dumi: Gwamnatin Edo ta dakatar da ASUU, ta ba da umarnin a cigaba da karatu - Dimokuradiyya

Gwamnatin jihar Edo ta dakatar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), da sauran kungiyoyi Makamancinta a duk manyan makarantun jihar.

Hakan ya biyo bayan Tattakin da daliban jami’ar Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma suka yi kan yajin aikin da kungiyar ASUU ta shiga, a cewar wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Osarodion Ogie ya fitar ranar Laraba.

Ogie ya bayyana cewa an cimma wannan matsayar ne bayan taron majalisar zartarwar jihar a gidan gwamnati dake birnin Benin.


Download Mp3

“Ta wannan sanarwar, za a ci gaba da ayyukan ilimi a dukkannin Makarantu mallakar gwamnatin jihar, kuma an umurci dukkan ma’aikatan da su koma bakin aikinsu,” in ji shi.

“Dalibai a duk manyan makarantun gwamnati ana sa ran za su dakoma karatu kamar yadda aka dauki matakan da suka dace don ganin an dawo da ayyukan ilimi.

“An umurci hukumomin da abin ya shafa su biya dukkan albashin da ba a biya ba nan take.

“An umurci hukumar gudanarwar jami’ar ta Ambrose Alli da ke Ekpoma da su aiwatar da dokar, da bayyana guraben aiki da kuma tallata matsayin duk wani ma’aikacin da ya ki komawa bakin aiki bisa ga wannan umarnin.”t

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy