Da Dumi-Dumi: Jam’iyar PDP ta nada sabon shugaban marasa rinjaye na majalissar dattijai

0

Da Dumi-Dumi: Jam’iyar PDP ta nada sabon shugaban marasa rinjaye na majalissar dattijai - Dimokuradiyya

Jam’iyyar PDP ta tsayar da Sanata Philip Aduda a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Haka kuma an zabi Sanata Chukwuka Utazi (Enugu ta Arewa) a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye a majalissar.

Nadin na kunshe ne a wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyawu.


Download Mp3

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a farkon zaman majalisar.

Nadin Aduda ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu).

Abaribe, a makon da ya gabata, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa All Progressives Grand Alliance (APGA).

Har ila yau, jam’iyyar PDP a cikin wasikar da ta aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ta bayyana cewa Sanata Utazi ya nada shi a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye, sakamakon daukakar da Sanata Aduda ya yi a matsayin shugaban marasa rinjaye.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy