Da Dumi-dumi: Jiga-jigan Jam’iyyar APC Sun Isa Fadar Shugaban Kasa Villa Domin Ganawa Da Buhari

0

Da Dumi-dumi: Jiga-jigan Jam’iyyar APC Sun Isa Fadar Shugaban Kasa Villa Domin Ganawa Da Buhari - Dimokuradiyya

A yanzu haka dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana ganawa da ‘yan takarar jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari, wanda ya dawo daga taron ECOWAS na musamman da aka yi sa’o’i da suka wuce, zai gana da akalla mutane 23 da aka amince da su a matsayin wadanda suke neman tsayawa takarar shugabancin kasa.

Masu fatan tsayawa takarar shugabancin kasar dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Gwamna Yahaya Bello (Kogi), Dave Umahi (Ebonyi), Kayode Fayemi (Ekiti), tsohon ministan harkokin Neja Delta, Goodwill Akpabio, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da dai sauransu.

Yayin da ya rage sa’o’i 48 a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, taron zai ta’allaka ne kan zaben dan takarar bisa tsarin yarjejeniya.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa shugaban kwamitin tantancewar, Dr John Oyegun, a ranar Juma’a ya shaidawa manema labarai cewa kashi 99 cikin 100 na masu son tsayawa takara suna goyon bayan yarjejeniya.

Jam’iyyar ADC reshen jihar Zamfara ta kammala zabukan fitar da gwani na jam’iyyar a jihar, inda ta tabbatar da cewa jam’iyyar za ta zama jam’iyya mai mulki a jihar a shekarar 2023.


Download Mp3

Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Gusau, babban birnin jihar, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Kabiru Garba, ya bayyana cewa APC ta gaji kuma ba ta da cikakkiyar gogewar da za ta iya tafiyar da jihar Zamfara, inda ya ce jam’iyyar ADC za ta karbe jihar a 2023.

Shugaban ya ci gaba da cewa, matsalar rashin tsaro da tabarbarewar siyasa da ke addabar jihar za su isa al’ummar Zamfara su yiwa APC tawaye ta hanyar akwatin zabe a 2023.

Ina tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa ADC za ta kawo sauye-sauye masu kyau a jihar da za su iya kawo sakamako mai amfani idan aka zabe su a 2023.”

Da yake jawabi a wajen zaben, shugaban kwamitin zaben wanda hedkwatar jam’iyyar ADC ta kasa ta aiko jihar Malami S. Galma ya yabawa wakilan da suka gudanar da zaben cikin lumana.

Ya kuma bayyana zaben a matsayin sahihi, karbabbe kuma mai cike da adalci, inda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar ADC da su bada hadin kai domin samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

An zabi Jafar Salisu Gusau bisa hadin kai a matsayin mai rike da tutar jam’iyyar a jihar.

Sai dai kuma duk sauran mukaman da aka zaba su ma an yi su ne bisa yarjejeniya ban da mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya inda ‘yan takara biyu Aliyu Sani Tsafe da Yusuf Sani suka fafata.

Sai dai Aliyu Sani Tsafe ya samu kuri’u 18 inda aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da abokin hamayyarsa, Alhaji Yusuf Sani ya samu kuri’u shida.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy