Da-Dumi-Dumi: Majalissa ta yi watsi da kudurin neman soke sashe na 84(8) da Shugaba Buhari ya amince da shi

0

Da-Dumi-Dumi: Majalissa ta yi watsi da kudurin neman soke sashe na 84(8) da Shugaba Buhari ya amince da shi - Dimokuradiyya

Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin da ke neman sa majalisar ta yi watsi da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka kan gyaran da aka yi wa sashe na 84(8) na dokar zabe ta 2022.

Majalisar a zamanta karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase, ta umurci wanda ya gabatar da kudirin, Honorabul Ben Igbakpa, daga jihar Delta ya gabatar da kudurin “bi tsarin da ya dace.”

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan majalisar, jim kadan bayan kammala zaben fidda gwani, sun soki sashe na 84(8) na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima bayan da akasarin su suka kasa cin tikitin tsayawa takara domin samun damar komawa majalisar a zaben dake tafe.

Wannan ci gaban dai ya sanya akasarin ‘yan majalisar suka fusata, lamarin da ya sa wasu daga cikin su suka yi cecekuce da kan shugaban.

A wani labarin kuma na daban.

Yanzu-Yanzu: Buhari zai maye gurbin tsofaffin Ministoci, ya aika da sunayen wadanda ya zaba zuwa majalisar dattawa

Majalisar dattawan Najeriya ta samu amincewar majalisar zartarwa tare da gabatar da sunayen mutane shida a matsayin wadanda za su maye gurbin ministocin da suka yi murabus domin tsayawa takarar shugaban kasa.

A wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Ibrahim Lawan, ya karanta a ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wadanda aka nada za su maye gurbin tsoffin ministocin da suka yi murabus daga majalisarsa.

Wasikar ta kasance kamar haka: “A bisa sashe na 8 karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima, ina mika sunayen wadanda aka nada a matsayin ministoci domin tabbatar da su”

Wadanda aka sanya sunayen su sune:

Henry Ikechukwu Ikoh— daga jihar Abia

Umana Okon Umana daga — Akwa Ibom

Egwumakama Joseph Nkama — Jihar Ebonyi

Goodluck Nnana Opiah – Jihar Imo

Umar Ibrahim El-Yakub –daga.jihar Kano

Ademola Adewole Adegoroye – jihar Ondo

Odum Odih – daga Jihar Rivers

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy