Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari na ganawa da mambobin majalissar Zartaswa kafin ya shilla Rwanda

0

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari na ganawa da mambobin majalissar Zartaswa kafin ya shilla Rwanda - Dimokuradiyya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan mako da ke gudana a fadarsa dake Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Ministocin masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Niyi Adebayo; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Mai shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami.

Sauran sun hada da ministar kudi, Dr Zainab Ahmed; Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi; Ministan Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello; karamin mai kula da masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Mariam Katagum, karamin ministan muhalli, Sharon Ikeazor, da dai sauransu.

Bayan taron da yammacin ranar Laraba, shugaban zai tashi daga Abuja zuwa Kigali na kasar Ruwanda, domin halartar taron kungiyar kasashen renon Ingila karo na 26, wanda zai gudana daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Yuni, 2022.

A wani labarin mai kama da wannan kuma.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Kigali na kasar Rwanda, a yau Laraba.

Buhari Zai je ne domin halartar taron kungiyar kasashe renon Ingila karo na 26 (CHOGM), wanda zai gudana daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa yau Laraba a Abuja.

A cewar Adesina, shugaban zai bi sahun sauran shugabannin domin tattaunawa kan ci gaba da wadata fiye da mutane biliyan biyu da ke zaune a kasashe 54 masu cin gashin kansu na Afirka, Asiya, Amurka, Turai da Pacific da suka hada da Commonwealth.

“Ana sa ran shugabannin kasashen za su sake jaddada aniyarsu na tabbatar da Yarjejeniya ta kasashe masu tattalin arziki, wadda ta mayar da hankali kan dimokuradiyya, ‘yancin dan adam, bin doka da oda, da kuma samar da damar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa,” in ji shi.

Shugaban na Najeriya, a cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, zai halarci bikin bude taron a hukumance a ranar 24 ga watan Yuni, sannan kuma za a gudanar da babban taron shugabannin kasashe da na gwamnatoci a ranar Juma’a 24 da Asabar 25 ga watan Yuni.

Ya ce: “Ana sa ran shugabannin za su yi la’akari da batutuwa da dama da suka hada da dawo da tattalin arzikin bayan COVID-19, dorewar bashi, sauyin yanayi, rage fatara, sana’o’in matasa da ayyukan yi, kasuwanci da samar da abinci.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy